Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza ma'adanar makaman Boko Haram a Borno (Bidiyo)

Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza ma'adanar makaman Boko Haram a Borno (Bidiyo)

Rundunar sojin saman Najeriya ta kai wa wani yanki da mayakan Boko Haram ke amfani da shi hari.

Dakarun sun yi wa yankin Parisu da ke dajin Sambisa a jihar Borno ruwan wuta ta sama, jaridar The Nation ta gano hakan.

Wannan harin da dakarun suka kai ya tarwatsa wurin ajiyar makaman mayakan Boko Haram din.

An yi nasarar halaka wasu daga cikin 'yan ta'addan kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Kamar yadda takardar da ta fito daga shugaban fannin yada labarai na hukumar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya ce sun kai harin ne bayan bayanan sirrin da suka samu a kan 'yan ta'addan.

Kamar yadda takardar ta bayyana: "A cikin kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin arewa maso gabas na kasar nan, rundunar sojin saman Najeriya ta ragargaza wasu 'yan ta;adda da kuma makamansu.

KU KARANTA: COVID-19: Kasashe 5 da cutar Korona ta fi tsananta, yawan mace-mace da waraka

"Al'amarin ya faru ne a yankin Parisu da ke dajin Sambisa na jihar Borno. 'Yan ta'adda da yawa sun rasa ransu a harin ranar 30 ga watan Afirilun 2020."

Kamar yadda yace, "An kai harin ne bayan samun bayanan sirri daga majiya mai karfi a kan harkokin 'yan ta'addan da yankin da suke."

Kamar yadda aka hango ta jiragen sama na yakin, an ga yankin da 'yan ta;addan suke kwana da kuma wuraren ajiye makamansu.

"Rundunar sojin saman Najeriyan za ta ci gaba da kokarin ganin bayan makiyan kasar nan har sai zaman lafiya ya tabbata a dukkan sassan kasar nan," yace.

A wani labari na daban, hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta ce dakin gwajin coronavirus na biyu a jihar Kano ya kammala.

Hukumar ta sanar da hakan ne ta shafinta na twitter a ranar Alhamis. Hukumar ta ce dakin gwajin na nan a jami'ar Bayero da ke Kano.

"Dakin gwaji na 18 a kasar nan ya kammala a jami'ar Bayero da ke Kano. Shine na biyu a jihar.

"Mun mayar da hankali wajen samar da dakunan gwajin cutar kamar yadda dabarun gwaji suka bayyana," wallafar tace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel