Wasu gwamnoni na siyasantar da lamarin cutar korona domin samun kudi daga gwamnatin tarayya - Dattawan Arewa

Wasu gwamnoni na siyasantar da lamarin cutar korona domin samun kudi daga gwamnatin tarayya - Dattawan Arewa

Kungiyar NEF ta dattawan Arewa, ta zargi wasu gwamnonin jihohi na Najeriya da laifin siyasantar da lamarin annobar cutar korona wadda ta barke a kasar.

Cikin sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis, ta lura cewa wasu gwamnoni a kasar ba sa kwatanta gaskiya yayin bayyana adadin mutanen da cutar korona ta kama a jihohinsu.

Sanarwar da ta fito daga bakin shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi, ya ce gwamnonin na kitsa wannan tuggu ne da manufa ta jawo hankalin gwamnatin tarayya domin samun kudade daga wurinta.

Haka kuma manufar wannan tuggu ta rashin kamanta gaskiya a kan adadin wadanda cutar korona ta harba ita ce janyo hankali kasashen ketare domin samun gudunmuwa.

Ya ce "kungiyar tana bakin cikin yadda gwamnoni da dama ke sharara karya kan adadin wadanda cutar korona ta harba a jihohinsu saboda tsammani da kuma sa ran samun wasu kudade daga gwamnatin tarayya da kuma gudunmuwar kasashen waje."

Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa; Farfesa Ango Abdullahi
Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa; Farfesa Ango Abdullahi
Asali: Depositphotos

"Sanin kowa ne cewa abin da kasar nan ta ke bukata a yanzu shi ne kyawawan manufofi na kare dukkanin 'yan Najeriya ta hanyar samar da wadatattun kayan aiki a wuraren gwajin gano masu cutar da ingatattun magunguna."

KARANTA KUMA: Sojoji sun kama Kanal da Manjo na bogi a Legas

"Akwai kuma bukatar gwamnati ta yi tanadin matakan bayar da tallafi ga mabukata wadanda dokar kulle da hana fita za ta jefa su cikin ha'ula'i da kangin kakanikayi."

Dole ne a yi watsi da manufofin da ke dakile ci gaban al'umma a wasu sassan kasar da kuma manufofin da ke barazanar danne hakkin rukunin mutane masu rauni."

"Jihohi su yi riko da manufofi mafi dacewa da yanayinsu, amma kuma manufofin su kasance sun karbu a kasa baki daya tare da shimfida matakan kare dukkanin al'umma."

"Musamman a yanzu mun yaba da hukuncin gwamnati na tura tawagar kwararru domin gano musabbabin yawan mace-macen da ake samu a Kano da kuma tallafawa gwamnatin jihar a fafutikar da ta ke yi na dakile yaduwar cutar korona."

A makon nan ne dai gwamnatin tarayya ta zargi gwamnonin Najeriya da yin gasa da 'yar rige-rige a tsakaninsu, yayin fayyace adadin mutanen da cutar korona ta harba a jihohinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel