COVID-19: Cutar Korona ta sake kama mutum 80 a jihar Kano

COVID-19: Cutar Korona ta sake kama mutum 80 a jihar Kano

Sakamakon gwajin ranar Alhamis ya tabbatar da kamuwar mutum 80 a jihar Kano.

Hakan ne ya kai jimillar masu cutar a jihar zuwa 219 inda ta sha gaban babban birnin tarayya na Abuja.

A halin yanzu, jihar Kano ce jiha ta biyu da ta fi kowacce yawan masu cutar Korona a Najeriya.

Hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta ce an tabbatar da kamuwar mutum 204 a jiya Alhamis a fadin kasar nan.

Hakan ne yasa jimillar masu cutar suka kai 1932 a Najeriya. Mutum 58 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da majinyata 319 suka warke kuma aka sallamesu.

Samun mutum 80 cif da suka harbu da cutar a jihar Kano ya matukar girgiza jama'a.

Wannan ce ranar da aka samu sakamako mafi muni tunda aka fara gwajin cutar a jihar.

COVID-19: Cutar Korona ta sake kama mutum 80 a jihar Kano
COVID-19: Cutar Korona ta sake kama mutum 80 a jihar Kano. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Mahaifi ya hana dansa shiga gida bayan ya dawo daga jihar Legas (Bidiyo)

Jihar Legas na biye da Kano a baya inda aka samu mutum 45. A jihar Gombe an samu karin mutum 12, a Bauchi an samu karin 9, Sokoto akwai 9, Borno akwai 7, Edo akwai 7 sai jihohin Ribas da Ogun an samu karin shida-shida.

A babban birnin tarayya, Akwa Ibom da Bayelsa an samu karin mutane hurhudu yayin da aka samu karin mutum 3 a Kaduna.

A jihohin Oyo, Delta da Nasarawa an samu karin mutum bibbiyu.

A jihohin Ondo da Kebbi kuwa an samu karin mutum daidai.

Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta tabbatar da cewa jihohi 34 ne cutar ta bulla a Najeriya a ranar Alhamis.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu ya ce shi da gwamnatinsa na tare da jama'ar jihar kuma ba za su basu kunya ba.

A takardar da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya ce makomar binciken da ake yi a yanzu a jihar ne zai bayyana silar mace-macen.

Takardar ta ce: "Babu wani bacin lokaci da za mu tsaya yi a kan siyasa. Ba ga tsoffin masu mulki a matakin jiha ko tarayya ba, duk babu banbanci.

"Wannan ba lokacin magana bane. Manufar dukkanmu shine tseratar da rai da lafiyar 'yan kasa. Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa na tare da jama'ar jihar Kano kuma ba za su basu kunya ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel