An sake kama 'yan gudun hijira a cakude da dabbobi suna kokarin shiga Kaduna daga Kano (Hotuna)

An sake kama 'yan gudun hijira a cakude da dabbobi suna kokarin shiga Kaduna daga Kano (Hotuna)

An kama wasu manyan motocin dako guda biyu da aka boye mutane a cikinsu a yayin da suke kokarin shiga jihar Kaduna ta kan iyakarta da jihar Kano.

An cakuda mutane da dabbobi domin yin basaja wajen shigar da su jihar Kaduna. Wannan ba shine karo na farko da aka samu mutane a boye a cikin manyan motocin dako suna kokarin shiga jihar Kaduna daga Kano ba.

A cikin sanarwar da kwamishinan harkokin cikin gida a jihar Kaduna ya fitar, ya bayyana cewa, "mun samu labarin cewa wasu manyan motocin dako sun shigo har Gwargwaji a Zariya, jihar Kaduna, daga Kano.

"Mun yi nasarar cafkesu a yankin karamar hukumar Zariya a yunkurinsu na son shigowa jihar Kaduna.

"An yi hikima da wayon boye mutane a cikin dabbobi, wasu tarkacen kaya da baburan hawa. Amma duk da haka mun yi nasarar ganosu, kuma mun tursasu komawa inda suka fito, kamar yadda dokar jihar Kaduna a tanada.

"Jami'anmu na aikin tabbatar da dokokin jiha a kan iyakokinmu, kuma suna kama fasinjoji tare da rakasu kan iyakar jihar da suka fito.

Hana shiga jihar Kaduna na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta dauka domin dakile yaduwar annobar covid-19.

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa labarin cewa jami'an tsaro tare da hadin gwuiwar jami'an gwamnatin Kaduna sun kama wasu manyan motocin dakon kayan abinci da aka boye mutane a cikinsu.

An kama motocin ne a kauyen Sabon Gida da ke yankin karamar hukumar Ikara yayin da suke kokarin shiga jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: A cikin kasa da sati uku, Kano ta zama ta biyu a yawan ma su cutar covid-19 a Najeriya

Manyan motocin sun yi yunkurin shiga jihar Kaduna ne ta iyakarta da karamar hukumar Kiru ta jihar Kano.

Motocin sun yi basaja a zuwan sun dauko kayan abinci ne da zasu kai jihar Kaduna.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar Kaduna, ya ce jami'an tsaro sun kama motocin yayin da suke rangadin tabbatar da dokar hana zirga-zirga.

"Sun sabawa dokar hana zirga-zirga, kamar yadda kowa zai iya gani. Mun samu mutane da yawa da aka boye a cikin manyan motocin.

"Mun yi nasarar kamasu kafin su shiga cikin jihar Kaduna, kuma za mu mayar dasu inda suka fito," a cewar Aruwan.

An sake kama 'yan gudun hijira a cakude da dabbobi suna kokarin shiga Kaduna daga Kano (Hotuna)

'Yan gudun hijira a cakude da dabbobi
Source: Facebook

An sake kama 'yan gudun hijira a cakude da dabbobi suna kokarin shiga Kaduna daga Kano (Hotuna)

'Yan gudun hijira suna kokarin shiga Kaduna daga Kano
Source: Facebook

An sake kama 'yan gudun hijira a cakude da dabbobi suna kokarin shiga Kaduna daga Kano (Hotuna)

An sake kama 'yan gudun hijira a cakude da dabbobi suna kokarin shiga Kaduna daga Kano
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel