Mace-mace a Kano: shugaban kwamitin shugaban kasa dake yaki da COVID-19 ya rasa mahaifinsa

Mace-mace a Kano: shugaban kwamitin shugaban kasa dake yaki da COVID-19 ya rasa mahaifinsa

Shugaban kwamitin shugaban kasa dake yaki da annobar COVID-19, wanda aka fi sani Coronavirus, Dakta Sani Aliyu ya rasa mahaifinsa, Alhaji Aliyu Daneji.

Jaridar Punch ta ruwaito Alhaji Daneji ya rasu ne a daren Laraba a jahar Kano yana da shekara 96 a duniya.

KU KARANTA: Mace mace a jahar Kano: Mutane 2 sun mutu dalilin cutar Coronavirus

Guda daga cikin yayansa, Mahmud Daneji ne ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasu, ina yace marigayim ya rasu ne bayan fama da jinya na dan karamin lokaci.

Da safiyar Alhami, 30 ga watan Afrilu aka gudanar da jana’izarsa a Sabuwar Kofa dake kusa da makarantar Firamari ta Kwalli, cikin birnin Kano, daga nan kuma aka binne shi.

Marigayi Aliyu Daneji ya taba zama babban sakatare a ma’aikatar kudi ta jahar Kano daga shekarar 1972 zuwa shekarar 1975.

Mace-mace a Kano: shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19 ya rasa mahaifinsa
Aliyu Daneji Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

A ranar Talata ne Dakta Sani Aliyu ya jagoranci tawagar kwararru zuwa jahar Kano domin su taimaka ma gwamnatin jahar wajen yaki da annobar Coronavirus wanda ta yi kamari a jahar.

A hannu guda ma’aikatar kiwon lafiya ta gwamnatin jahar Kano ta sanar da karin mutuwar mutane 2 a sakamakon cutar COVID19 wanda aka fi sani da suna annobar Coronavirus.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito ma’aikatar ta bayyana haka ne cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na kafar sadarwar zamani na Twitter, a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu.

Hakan ya kawo adadin mutanen da suka kamu da cutar a jahar Kano zuwa 139 daga fara samun bullar cutar zuwa karfe 12:05 na daren Alhamis.

A wani labari kuma, har yanzu ana cigaba da samun wadannan mace mace duk da matakin da gwamnatin jahar da ta tarayya suka ce suna dauka game da lamarin.

Daily Trust ta ruwaito a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu ma an sake samun ire iren mace macen nan a jahar Kano, inda wasu manyan mutane guda uku suka mutu a rana daya.

Wadannan mutane uku da suka mutu sun hada da Alhaji Salisu Ado, Alhaji Aminu Yahaya da kuma Alhaji Muhammad Aliyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel