Mace-macen Kano: Ba zan ci amanar Kanawa ba - Buhari

Mace-macen Kano: Ba zan ci amanar Kanawa ba - Buhari

A yayin da hukumomi ke kokarin gano musabbabin mace-macen da ke faruwa a jihar Kano, Shugaban kasa Muhammadu ya ce shi da gwamnatinsa na tare da jama'ar jihar kuma ba za su basu kunya ba.

A takardar da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya ce makomar binciken da ake yi a yanzu a jihar ne zai bayyana silar mace-macen.

Takardar ta ce: "Babu wani bacin lokaci da za mu tsaya yi a kan siyasa. Ba ga tsoffin masu mulki a matakin jiha ko tarayya ba, duk babu banbanci.

"Wannan ba lokacin magana bane. Manufar dukkanmu shine tseratar da rai da lafiyar 'yan kasa. Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa na tare da jama'ar jihar Kano kuma ba za su basu kunya ba.

"Ganin abinda ke faruwa a Kano, akwai bukatar gwamnatin tarayya da ta jihar Kano sun hada kai wajen samo mafita tare da tabbatar da su a jihar.

"A halin yanzu, ana binciken sila ko tushen mace-macen a jihar Kano don gano kan lamarin.

"A yayin da wasu suke tunanin hawan jini, ciwon sukari, sankarau da cutar zazzabin cizon sauro ke kawo mace-macen, wasu na zargin cutar COVID-19.

“Akwai bukatar mu zauna a shirye don rungumar sakamakon da zai bayyana."

Mace-macen Kano: Ba zan ci amanar Kanawa ba - Buhari
Mace-macen Kano: Ba zan ci amanar Kanawa ba - Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Budaddiyar wasikar Kwankwaso: Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi

"Makonni kadan kenan da Najeriya ta fara wannan yakin da makiyin da ba a gani wanda ya gallabi kusan kowacce kasa.

"A cikin kwanakin nan ne WHO ta bayyana cewa yanzu nahiyar Afrika ta fara yakin nan.

"Akwai abubuwa masu yawa da bamu sani ba game da cutar. Abinda kadai muka sani shine yadda cutar ke yaduwa a duniya a kowacce rana.

"Mun san cewa akwai karancin kayayyakin kariya a duk fadin duniya, rashin kayan gwaji da sauran abubuwan bukata don yakar cutar," yace.

Kamar yadda takardar ta bayyana, sanannen abu ne idan aka ce akwai wuraren da cutar ta fi kamari a Najeriya.

"Wannan ba lokacin bata wa bane wajen cimma manufofin siyasa ba. Koda ka kasance tsohon dan siyasa a matakin jiha ko na tarayya, wannan ba lokacin surutu bane.

"Dukkanmu neman mafita muke yi don tseratar da rayuka da lafiyar 'yan kasa," Garba Shehu yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel