Yan bindiga sun kai ma Yansanda harin kwantan bauna a Kaduna, sun kashe 1, saura sun jikkata

Yan bindiga sun kai ma Yansanda harin kwantan bauna a Kaduna, sun kashe 1, saura sun jikkata

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kashe wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya mai mukamin Inspekta a garin Falwaya dake kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Yan bindigan sun kai harin kwantan bauna ne a kan wata motar Yansanda dake tafiya da yammacin Litinin, 27 ga watan Afrilu a kan hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

KU KARANTA:Majalisa ta amince ma Buhari ya sake antayo ma Najeriya bashin N850,000,000,000

Wani dan banga dake yankin, Hussaini Imam ya shaida ma Daily Trust cewa jami’in dansandan da aka kashe yana aiki ne a ofishin Yansanda dake Buruku, cikin karamar hukumar Chikun.

Hussaini ya ce yan bindigan sun sake kai wani samame a kauyen Udawa dake karamar hukumar Chikun a ranar Talata, inda suka yi awon gaba da dakacin kauyen.

Yan bindiga sun kai ma Yansanda harin kwantan bauna a Kaduna, sun kashe 1, saura sun jikkata
Yan bindiga sun kai ma Yansanda harin kwantan bauna a Kaduna, sun kashe 1, saura sun jikkata
Asali: Depositphotos

“Bayan sun kashe Sufeta Dantani, tare da jikkata abokan aikinsa a ranar Litinin, yan bindigan sun karasa zuwa wani kauyen Udawa inda suka yi awon gaba da dakacin kauyen tare da wasu mutane 5, sa’anann suka kashe wani mutum mai suna Lado” Inji shi.

Ko da majiyar mu ta tuntubi rundunar Yansandan jahar, sai Kakaakin rundunar, ASP Mohammed Jalige ya ce bai samu labarin harin ba.

A wani labarin kuma, kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta musanta ikirarin da shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya yi na cewa ya fatattake su daga yankin tafkin Chadi.

Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wani bidiyo da ta saka inda ta nuna yadda ta yi ma jami’in Sojan kasar Chadi kisan gilla ta hanyar dirka masa harsashi a kai.

Jami’an gwamnatin kasar Chadi sun tabbatar da sahihancin bidiyon. Ko a cikin bidiyon an hangi mutumin da yan ta’addan suka kashe yana sanye da kakin Sojojin Chadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel