Covid-19: Ma su karya doka za su biya tarar N5,000, N10,000, N20,00 da N30,000 - Gwamnan Bauchi

Covid-19: Ma su karya doka za su biya tarar N5,000, N10,000, N20,00 da N30,000 - Gwamnan Bauchi

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rattaba hannu a kan dokokin dakile yaduwar cututtuka ma su yaduwa a jihar Bauchi.

An kirkiri dokokin ne domin kawo karshen yaduwar annobar cutar covid-19 a jihar Bauchi.

"Kafin wannan lokaci, mun saka wasu dokoki da suka hada da takaita zirga - zirga, rufe kasuwanni, haramta achaba, dakatar da taron jama'a da takaita adadin mutanen da babur mai kafa uku da motocin haya za su dauka

"Mun dauki wadannan matakai domin alhakin kare lafiyar jama'a ya rataya a wuyanmu duk da mun san yin hakan ya takura jama'a. Amma, dole ne mu dauki duk wasu matakai domin rayukan jama'ar jihar Bauchi.

"Wadanda aka samu suna karya dokar zaman gida, kin amfani da takunkumin rufe fuska da 'ma su yin acahaba zasu biya tarar N5,000.

"Ma su karya dokar nesanta zasu biya tarar N5,000, motocin haya, a cikin jihar Bauchi, da basu bi tsarin nesanta ba zasu biya tarar N10,000, yayin da motocin hayar da suka shigo daga wasu jihohin za a ci tararsu N20,000, manyan motocin dako kuma za a ci tararsu N30,000," a cewar gwamnan jihar Bauchi.

A cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na tuwita, ya ce, dokar, wacce ya rattaba hannu a kanta a yau, Talata, za ta fara aiki ne nan take.

Covid-19: Ma su karya doka za su biya tarar N5,000, N10,000, N20,00 da N30,000 - Gwamnan Bauchi

Bala Mohmamed; Gwamnan Bauchi
Source: UGC

Sabbin dokokin na gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyarsa ta PDP ta yi zargin cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai fadi wani abu da ya yiwa 'yan Najeriya dadi ba a cikin jawabin da ya gabatar kai tsaye da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Sheikh Yola da sauran manyan mutane uku da aka yi jana'izarsu a Kano ranar Talata

Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi ne domin sanar da 'yan Najeriya halin da ake ciki dangane da yaki da annobar covid-19 a fadin kasa tare da sanar da daukan sabbin matakai a kan yanayin da ake ciki.

A cikin jawabin da sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan, ya fitar a daren ranar Litinin, PDP ta ce shugaba Buhari bai zo da wani abu sabo a cikin jawabinsa ba.

PDP ta ce Buhari ya kara jaddada dokar rufe jihohi ne kawai, amma ba tare da yin bayani a kan yadda za a taimaki jama'a da masana'antun da tattalin arzikinsu ya karye saboda dokar ba.

A cewar PDP, fatan 'yan Najeriya shine samun mafita daga halin da kasa ta fada ciki, amma duk da haka ba a ji Buhari ya ambaci wata hanya da za a fitar da 'yan Najeriya daga wahala ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel