COVID-19: Martanin jama'ar jihar Kano a kan hukuncin Buhari

COVID-19: Martanin jama'ar jihar Kano a kan hukuncin Buhari

Wasu mazauna birnin Kano sun bayyana goyon bayansu a kan dokar hana walwala da shugaban Buhari ya saka wa jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, a ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada sanarwar rufe jihar saboda annobar Coronavirus.

Shugaban ya ce: "A dangane da jihar Kano, na bada umarnin rufe ta gaba daya na makonni biyu tun daga yanzu.

"Gwamnatin tarayya za ta tura duk wani abu da ake bukata don shawo kai da hana yaduwar annobar zuwa jihohin da ke makwabtaka da Kano."

A tattaunawa ta daban-daban da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya yi da mazauna garin, sun bayyana cewa wannan babban ci gaba ne.

Habibu Umar, mazaunin yankin Rijiyar Zaki da ke birnin Kano, ya ce wannan hukuncin ne mafi cancanta ballantana wajen tsayar da yaduwar cutar.

Umar ya ce sakamakon rashin bin dokar hana zirga-zirga da nisantar juna da aka yi a jihar da farko, hakan ne ya kawo bukatar rufe jihar kwata-kwata.

"Mace-macen da ake ta yi a jihar ne yasa dole a dauka matakin gaggawa don kare lafiyar jama'a da hana yaduwar cutar," ya kara da cewa.

Wani mazaunin jihar mai suna Usman Baballe, ya ce zai yi matukar farin ciki da aka saka wannan dokar amma idan an biya ma'aikata albashinsu.

"Za mu zauna a gida kuma za mu kiyaye dokoki tare da yin addu'ar karshen wannan annobar," yace.

Baballe ya jinjinawa kwamitin yaki da cutar na fadar shugaban kasa sakamakon kokarinsu na hana yaduwar cutar a jihar.

COVID-19: Martanin jama'ar jihar Kano a kan hukuncin Buhari
COVID-19: Martanin jama'ar jihar Kano a kan hukuncin Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Sabbin dokokin El-Rufa'i na kullen jihar Kaduna

Hakazalika, Aminu Ibrahim mazaunin jihar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da adalci wajen rabon tallafin ga masu karamin karfi.

Ibrahim ya ce kullen ya kai masu nema ga matukar takura don haka akwai bukatar tallafi don jama'a su zauna a gida.

Ya kara da kira ga jama'ar jihar da su kiyaye shawarwarin masana kiwon lafiya don hana yaduwar cutar a jihar.

Ibrahim ya yi kira ga mazauna jihar da su kiyaye dokokin nisantar juna tare da kiyaye tsaftar jiki.

Kamfanin Dillancin Labarai ya bayyana cewa, a ranar 14 ga watan Afirilu ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe jihar na kwanaki bakwai don hana yaduwar Covid-19.

An sabunta dokar kullen na mako daya ne bayan an bude jihar na sa'o'i 12 a ranar 23 ga watan Afirilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel