Yanzu-yanzu: Buhari ya saka dokar hana fita na tsawon makonni biyu a jihar Kano

Yanzu-yanzu: Buhari ya saka dokar hana fita na tsawon makonni biyu a jihar Kano

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin sanya dokar hana fita gaba daya a jihar Kano na tsawon makonni biyu fari daga yanzu.

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi ma kasa ranar Litinin.

Ya ce ya yanke shawarar sanya wannan dokar a jihar Kano ne bisa ga irin mace-macen da ke faruwa a jihar da har yanzu ba'a gane dalilin ba.

Yace: "Game da Kano, na bada umurnin kafa dokar hana fita gaba daya na tsawon makonni biyu fari daga yanzu."

"Gwamnatin tarayya za tayi dukkan iyakan kokarinta na kudi, kayan aiki da ma'aikata wajen taimakawa jihar wajen takaita yaduwar cutar a jihar da kuma zuwa wasu jihohin dake makwabta."

KU KARANTA: Sabbin Mutane 12 sun kamu da Coronavirus a Sokoto da Taraba

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita dokar hana fitar da ya kakabawa al'ummar birnin tarayya Abuja, jihar Legas da Ogun, da tsawon mako daya.

Shugaban kasan ya sanar da hakan ne a jawabin da yayi ga yan kasa karo na uku kan lamarin annobar Korona.

Yace:"Dokar hana fita a FCT, Legas da Ogun zai cigaba da kasancewa zuwa ranar 4 ga Mayu, 2020."

Amma daga ranar 4 ga Mayu, Buhari ya bayyana cewa za'a fara sassauta dokar hana fitar a wadannan garuruwan.

Yace: "Bisa ga shawarwarin da kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19, kwamitocin duba illan lamarin ga tattalin arzikin kasa da kungiyar gwamnonin Najeriya, na bada umurnin saukaka dokar hana fita a FCT, Legas da Ogun fari daga ranar Litnin, 4 ga Mayu, 2020."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel