Cutar korona ta hallaka mutane 2 a jihar Kano

Cutar korona ta hallaka mutane 2 a jihar Kano

Mun samu rahoton cewa, mahukuntan lafiya a jihar Kano sun sanar da karin mutane biyu da cutar korona ta hallaka a jihar.

A halin yanzu dai cutar korona ta yi sanadiyar ajalin mutane uku a jihar.

Ma'aikatar lafiyar jihar ce ta sanar da hakan da misalin karfe 12.15 na ranar Litinin, 27 ga Afrilun 2020 a kan shafinta na Twitter.

Har yanzu dai babu wani sauyi da aka samu na yawan adadin wadanda cutar korona ta harba a jihar Kano daga mutum 77 kamar yadda hukumar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC ta sanar a ranar Lahadi.

Taskar bayanai ta NCDC ta tabbatar da cewa, a halin yanzu dai mutane 1273 cutar corona ta harba a duk fadin Najeriya.

Har ila yau kuma jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan wadanda cutar ta kama inda adadinsu ya kai 731, sai kuma birnin tarayya inda cutar ta harbi mutum 141 yayin da jihar Kano ta biyo baya da mutum 77.

Duka dai a fadin Najeriya, an samu mutum 40 wadanda mai yankan kauna ta katsewa hanzari bayan sun kamu da cutar korona.

Bayan annoba korona da zama ruwa dare a duk fadin duniya, al'ummar jihar Kano na zaune cikin fargaba saboda yawan mace-macen da dattawa a jihar ke yi a 'yan kwanakin nan.

A ranar Asabar kadai, fiye da mashahuran mutane 10 'yan asalin jihar Kano sun riga mu gidan gaskiya, ciki har da editan babban kamfanin jaridar nan na Triumph, Musa Tijjani.

KARANTA KUMA: Coronavirus: An kamo mutumin da ya gudu daga cibiyar killacewa a Borno

Sauran mashahuran mutanen da ajali ya cimma a ranar Asabar din sun hadar da; Farfesa Ibrahim Ayagi, Dr. Musa Gwarzo, Dahiru Rabiu, Adamu Dala, Salisu Lado, Shamsiyya Mustapha, Nene Umma, Garba Fagge, Nasiru Bichi, Farfesa Aliyu Umar Dikko da kuma Aminu Yahaya.

Haka kuma a ranar Lahadi, mun samu rahoton cewa wasu manyan mutane biyu a jihar Kano sun rasa rayukansu sanadiyar wata bakuwar cuta da hakan ya sake jefa tsoro a zukatan al'umma.

Mutanen biyu wadanda mai yankan kauna ta katsewa hanzari a ranar Lahadin sun hadar da tsohon kwamishinan ilimi na jihar, Alhaji Aminu Yahaya, da kuma wani farfesan nazarin aikin jarida na jami'ar Bayero, Farfesa Balarabe Maikaba

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, ko a makon da ya gabata, an binne gawawwakin kimanin mutane 150 a cikin birnin Kano sanadiyar wannan bakuwar cutar, lamarin da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ya ci tura.

Da dama dai ana zargin cewa annobar cutar korona ce ke hallaka mutane a Kano. Sai dai, kamar yadda kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba ya bayyana, mutane na mutuwa ne daga cututtuka irinsu sankarau, hawan jini, zazzabin cizon sauro, ciwon sukari da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel