Za mu karbi Shekau da hannu biyu idan ya mika wuya — Rundunar Sojin Najeriya

Za mu karbi Shekau da hannu biyu idan ya mika wuya — Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce za ta karbi shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau idan ya ajiye makamansa ya mika wuya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ta ce idan Shekau ya bi dokokin mika wuya yayin yaki ko tashin hankali, rundunar za ta karbe shi bisa tsarin irin wanda kasashen duniya suka amince a kai.

Shugaban sashin watsa labarai na sojojin, Manjo Janar Enenche ne ya bayyana hakan a ranar Jumaa yayin hirar da ya yi da Channels TV.

Idan Shekau ya mika wuya, za mu karbe shi — Rundunar Sojin Najeriya
Idan Shekau ya mika wuya, za mu karbe shi — Rundunar Sojin Najeriya
Asali: Twitter

Ya ce, "Kwararru sun yi nazarin bidiyon da Shekau ya fitar a baya bayan nan. Akwai rade radin cewa yana son ya mika wuya.

"Idan har da gaske yan taadan za su mika wuya, akwai tsarin da ake bi don yin hakan. Idan Shekau ya bi wannan dokokin ya mika kansa, za mu amince da mika wuyansa."

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19

A wani rahoton, mun kawo muku cewa Hedkwatan Tsaro ta Najeriya ta ce Dakarun Sojojin Saman ta karkashin Operation Lafiya Dole (OPLD), sun lalata wani gida da yan taaddan Boko Haram ke zaune a Bulawa kusa da dajin Sambisa a jihar Borno.

Mai kula da sashin watsa labarai na hedkwatan tsaron, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan cikin wata sako da ya fitar a shafin Twitter a ranar Alhamis a Abuja.

Enenche ya ce sojojin sun kai harin ne a ranar 21 ga watan Afrilu bayan samun bayanan sirri daga masu leken asiri da kuma amfani da naurar leken asiri ta zamani inda suka tabbatar yan taadan na gidan.

Ya yi bayanin cewa an yi amfani da jiragen yaki da Rundunar Sojin Saman Najeriya inda suka yi ruwan bama bamai a gidan suka kashe yan taadan tare da lalata gidan. A cewarsa, an kashe wasu daga cikin yan taadan da ke zaune a gidan yayin harin.

Ya ce, "An murkushe wasu daga cikin yan Boko Haram din da su kayi yunkurin neman mafaka domin su kai wa jirgin yakin NAF hari bayan tarwatsa gidan.

"Rundunar Sojojin Najeriya za ta cigaba da jajiracewa wurin aikin da ta sa a gaba na samar da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Gabas da kare Najeriya daga makiyan ta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel