NCDC ta tura tawagar kwararru domin tunkarar cutar korona a Kano

NCDC ta tura tawagar kwararru domin tunkarar cutar korona a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa, cibiyar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya , NCDC, ta tura wata tawagar kwararru 17 zuwa jihar Kano domin tunkarar annobar cutar corona.

Sashen Hausa na BBC ya tabbatar da cewa, bakwai daga cikin 'yan tawagar sun fito ne daga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

Babban wakili a kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin sa ido a kan cutar corona a Najeriya, Dr Aliyu Isah, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai.

Mun ji cewa yanzu an kai matakin da har an dakatar da gwajin gano masu cutar corona a Kano domin su kan su masu gwajin sun kamu da cutar kamar yadda Dr Sani ya bayyana.

Yana mai cewa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano ya rufe dakin gwajin cutar domin su kansu masu gwajin an gano cutar ta harbe su.

A Larabar makon nan da muke ciki, mun ji cewa an dakatar da gwajin gano wadanda cutar corona ta harba a sanadiyar rashin kayan aiki na aiwatar da gwajin.

Farfesa Sadiq Isah na kwamitin yaki da cutar corona a Kano, shi ne ya tabbatarwa manema labarai hakan da cewa dole ce ta sanya aka dakatar da gwajin don babu sinadaran da ake bukata domin ci gaba da gwajin.

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje
Asali: Twitter

Daga bisani kuma Farfesan ya shaidawa manema labarai cewa, an kai sinadaran gwaje-gwajen amma babu damar ci gaba da aiki a dakin gwajin har sai bayan kwanaki biyu.

Dalilin hakan kuwa shi ne an riga da yin feshin kashe kwayoyin cuta a dakin da sai bayan an dauki wani tsawon lokaci kana a shige sa.

KARANTA KUMA: Rundunar Sojin saman Najeriya ta kara inganta ayyukan gudanarwa na dakarunta

Sanadiyar rashin ci gaba da gwaje-gwajen a birnin Kano, ya sanya kwanaki biyu a jere mahukuntan lafiya a jihar ba su fitar da alkaluman wadanda cutar ta harba a Kanon ba.

Idan ba a manta ba a ranar 11 ga watan Afrilun 2020 ne ma'aikatar Lafiya a Kano ta sanar da bullar cutar karo na farko a jikin wani tsohon Kwamishinan jihar bayan dawowarsa daga Birtaniya.

Tun daga wannan lokaci dai likafar annobar ta ci gaba a sanadiyar yadda take yaduwa tamkar wutar daji.

Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya nemi gwamnatin tarayya da ta kawo dauki a fafutikar da gwamnatinsa ke yi na dakile yaduwar cutar.

Ganduje ya nemi gwamnatin tarayya ta agazawa jihar Kano da tallafin Naira biliyan 15 domin samun damar ci gaba da yakar cutar corona a jihar.

Mun ji cewa Gwamnatin Tarayyar dai ta bai wa jihar Legas tallafin kudi har naira bilyan 10.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel