Corona: Kotun tafi da gidanka ta kama mutane 500 da laifin karya dokar ta baci a Abuja

Corona: Kotun tafi da gidanka ta kama mutane 500 da laifin karya dokar ta baci a Abuja

Hukumar tafiyar da babban birnin tarayya Abuja, FCTA, ta sanar da kama akalla mutane 500 da laifin yi ma dokar zaman gida saboda Coronavirus karan tsaye.

Kamfanin dillancin labaru NAN, ta ruwaito hukumar ta yi amfani da kotunan tafi da gidanka ne wajen gurfanar da mutanen tare da hukuntasu ta hanyar zartar musu da hukunci nan take.

KU KARANTA: Sakamakon bincike: An bankado dabbar da ta yi sanadiyyar samuwar Coronavirus a duniya

Shugaban kwamitin dabbaka dokar ta baci a garin Abuja, Ikharo Attah ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a Abuja a ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu.

Attah ya bayyana damuwarsa da yadda mutane ke yi ma dokar hana shige da ficen karan tsaye, inda yace suna samun wannan matsala daga shuwagabannin addinai.

Sai dai yace yawancin mutanen da kotun suka yanke ma hukunci daga cikin mutane 500, sun kasance masu motoci ne dake fita yawo babu gaira babu dalili.

Corona: Kotun tafi da gidanka ta kama mutane 500 da laifin karya dokar ta baci a Abuja
Corona: Kotun tafi da gidanka ta kama mutane 500 da laifin karya dokar ta baci a Abuja
Asali: Twitter

Don haka Attah ya yi kira ga jama’an Abuja su daina yi ma umarnin gwamnati karan tsaye, musamman irin wannan umarni wanda aka bayar da shi don kare yaduwar cutar Coronavirus.

“Cutar nan babu ruwanta da girman mutum ko addininsa. Tun farkon zaman kotunan tafi da gidanka, sun yanke ma mutane fiye da 500 hukunci, yawancinsu an ci su tara ne, sa’annan aka sake su.

“An yi haka ne saboda tura su gidan yari zai zamo tamkar cin dunduniyar matakin da gwamnati take dauka na rage mutanen dake daure a kurkukun domin rage yaduwar cutar COVID-19. Yawancinsu kuma wannan ne karo na farko da aka taba samun su da laifi.” Inji shi.

A wani labari kuma, majalisar kiwon lafiya ta duniya, WHO, ta sanar da cewa an samu cutar COVID19, wanda aka fi sani da suna Coronavirus ne daga jikin Jemage.

Jaridar RFI ta bayyana cewa WHO ta tabbatar da hakan ne bayan wani bincike da ta kaddamar don ganon asalin cutar, inda sakamakon binciken ya nuna cewa daga jemage aka samo cutar.

A yanzu haka, wannan cuta mai toshe numfashin dan Adam ta kama mutane fiye da miliyan 2, kuma ta kashe mutum 160,000 a tsakanin kasashen duniya 170.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel