Da duminsa: Ma'aikatan asibiti 40 suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya

Da duminsa: Ma'aikatan asibiti 40 suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya

- Kwamitin shugaban kasa na yakar cutar Covid-19 ya ce yadda masu cutar ke karuwa a jihar Kano na ci gaba da tada musu hankali

- Ministan Lafiya ya bayyana adadin Likitoci da malaman jinyan da suka kamu da cutar

Ministan kiwon lafiyan Najeriya, Osagie Ehanire,ya bayyana cewa Ma'aikatan asibiti 40 suka kamu da cutar coronavirus a yayin ceto rayukan mutane.

Osagie Ehanire, ya bayyana hakan ne yayin hirar kwamitin kar-ta-kwanan fadar shugaban kasa kan yakar cutar Coronavirus da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Ya yi kira ga maaikatan lafiya su kula da kansu wajen jinyar marasa lafiya.

Da duminsa: Ma'aikatan asibiti 40 suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya
Likitin yakar Coronavirus a Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: Karyewar Mai: Jihohi na iya rasa kudin FAAC a Watan Yuni inji Gwamnan Gwamnoni

Shugaban Kwamitin, Boss Mustapha, ya ce yadda masu cutar ke karuwa a jihar Kano na ci gaba da tada musu hankali.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a Abuja a jiya yayin jawabi ga kwamitin.

Ya ce: "Halin da jihar Kano ke ciki abin tada hankali ne. Kwamitin na ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar don shawo kan lamarin.

"Kwamitin ya gano cewa ana ci gaba da samun masu cutar a kasar nan. Wannan kuwa ya danganta ne da yadda aka fadada wuraren gwajin."

Mustapha ya kara da cewa, ganin yadda lamarin ya sake yawaita, sun sauya sabbin tsarin gwaji don yanzu gida-gida ake bi don yin gwajin a jihohin Legas da Abuja.

Kamar yadda yace, gwaji, tantancewa, killacewa da kula da masu cutar ya zama dole in har ana bukatar takaita yawan masu kamuwa da cutar.

Ya mika godiyarsa ga sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta addinin musulunci a kasar nan a kan kwamitin fatawa ta gaggawa da ya kafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel