An nada Buhari gwarzon yaki da annobar cutar covid-19 a Afrika

An nada Buhari gwarzon yaki da annobar cutar covid-19 a Afrika

Shugabannin kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) sun nada shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a matsayin gwarzon da zai jagoranci yaki da annobar cutar covid-19 a yankin.

A ranar Alhamis ne shugabannin shiyya na ECOWAS su ka gudanar da taro ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ne ya sanar da nadin da aka yi wa Buhari a sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta (tuwita).

ECOWAS ta gudanar da taron ne domin tattaunawa a kan kokarin dakile yaduwar annobar covid-19 a kasashen da ke zaman mamba a kungiyar.

A cikin wata sanarwa da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa akwai kimanin mutum 5,774 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar covid-19 a yankin Afrika ta yamma.

Daga cikin adadin mutanen, mutum 1,616 sun warke, yayin da mutum 147 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon kamuwa da kwayar cutar covid-19.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya bayar da umarnin yin bulala ga duk wanda aka gani babu takunkumi a jiharsa

Ko a makon jiya, sai da kungiyar hadakar kasashen nahiyar Turai (EU) ta bawa Najeriya tallafin Yuro miliyan hamsin (£50m) domin yaki da annobar cutar covid-19.

Shugaban tawagar wakilan EU, Ambasada Ketil Karlsen, ne ya sanar da hakan yayin ziyarar da suka kai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa ranar Talata, 14 ga watan Afrilu.

Yayin ziyarar, tawagar wakilan ta mika sakon jinjinar EU ga shugaba Buhari a kan kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke yi na yaki da annobar covid-19.

Da yake gabatar da jawabi, shugaba Buhari ya mika godiyarsa ga EU a kan tallafin kudin da ta bawa Najeriya domin yakar annobar cutar covid-19.

Yawan kudin ya kai biliyan N21 idan aka juya shi zuwa kudin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel