Babban likita ya bayyana abin da yasa suka dakatar da gwajin Coronavirus a Kano

Babban likita ya bayyana abin da yasa suka dakatar da gwajin Coronavirus a Kano

Daraktan cibiyar nazarin cututtuka masu yaduwa na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Farfesa Isah Abubakar ya bayyana dalilin da yasa suka dakatar da gwajin Coronavirus a Kano.

Daily Trust ta ruwaito, Isah ya ce an dakatar da gwajin ne domin samun daman gudanar da wasu yan gyare gyare a cibiyar gwaje gwajen.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: An samu mutuwar mutum na farko a jahar Oyo

“Yana daga cikin tsarin mu gudanar da yan gyare gyare lokaci zuwa lokaci. Kamar yadda dokar mu ta tanada, cibiya irin wannan na bukatar feshi daga lokaci zuwa lokaci bayan an yi amfani da shi a tsawon wani lokaci.” Inji shi.

Sai dai Farfesa Isah ya musanta rahotannin dake cewa wai sun rufe cibiyar ne sakamakon karewar kayan aiki a cibiyar gwajin, inda yace:

“Mu na da kayan gwaji da dama, ban san me yasa jama’a ke son kawo rudani a cikin jama’a ba.”

Shi ma da yake jawabi, mataimakin daraktan aikin gwaje gwaje dake kula da cibiyar, Nasiru Magaji ya bayyana cewa suna sa ran bude cibiyar a ranar Juma’a domin cigaba da aiki.

Babban likita ya bayyana abin da yasa suka dakatar da gwajin Coronavirus a Kano

Babban likita ya bayyana abin da yasa suka dakatar da gwajin Coronavirus a Kano
Source: Facebook

“Mun yi ma dakin gwajin feshi ne, kuma zai dauke mu tsawon sa’o’i 48 kafin mu sake bude shi domin yin aiki. Don haka ba za mu bude shi ba sai bayan awanni 48.” Inji shi.

A ranar 11 ga watan Afrilun 2020 ne hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta hukumar, NCDC ta samar da cibiyar a Kano.

Sai dai al’ummar jahar Kano sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da isassun cibiyoyin gwaje gwajen Coronavirus a jahar don rage yaduwar cutar a yankin Arewacin Najeriya.

Wani mazaunin Kano, Shehu Muhammad ya ce: “Idan har jahar Legas za ta samu cibiyoyi guda 20, ban ga dalilin da zai sa Kano ba za ta samu fiye da cibiyoyi 20 ba, musamman yadda Kano ta fi legas yawan jama’a.”

A wani labarin kuma, majalisar lafiya ta duniya, WHO ta bayyana zuwa yanzu, Coronavirus ta kama mutane fiye da miliyan 2, kuma ta kashe mutum 160,000 a duniya gaba daya.

Shugaban WHO, Tedros Ghebreysus ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru game da annobar a ranar Laraba a birnin Geneva, kasar Switzerland.

“A duniya gaba daya, mutane miliyan 2.5 ne cutar COVID-19 ta kama, kuma an samu mace mace 160,000 a dalilin ta.” Inji shugaban WHO, Tedros Ghebreysus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel