COVID-19: Gwamnonin Arewa sun amince da haramta Almajiranci a yankin

COVID-19: Gwamnonin Arewa sun amince da haramta Almajiranci a yankin

Kungiyar gwamnonin Arewa ta daga kan cewa ya zama dole a haramta Almajiranci a yankin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da suke tattaunawa kan matakan da yankin za ta dauka don yaki da annobar coronavirus.

Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ne ya jagoranci taron da gwamnonin 17 suka gudanar ta hanyar amfani da yanar gizo.

A cewar Macham Makut, diraktan watsa labarai na Lalong, gwamnonin sun tattauna a kan cibiyoyin gwajin COVID-19 da ke yankin inda suka lura cewa akwai bukatar yin gyare gyare a wasu bangarorin.

Gwamnonin Arewa sun dage kan batun haramta Almajiranci
Gwamnonin Arewa sun dage kan batun haramta Almajiranci
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta fadi dalilan da yasa ta rufe kamfanin shinkafa na Tiamin

Har wa yau, gwamnonin sun amince da kafa a kalla wurin gwaji guda daya a kowane jiha domin saukaka gano masu dauke da cutar da kulawa da su.

Wani sashi na sanarwar ya ce, "A game da batun rufe iyakoki da dokar kulle, gwamnonin sun amince kowace jiha ta cigaba da saka dokokin da ya dace da jihar ta amma sun jadada rufe iyakokin jihohi domin takaita yaduwar cutar.

"Gwamnonin sun kuma tattauna hatsarin da Almajirai ke ciki sakamakon bullar coronavirus inda dukkansu suka amince a haramta almajiranci kuma a mayar da yaran zuwa gidajen iyayensu ko jihohinsu na asali.

"Sun dau alwashin cewa ba za su bari a cigaba da almajirancin ba duba da irin kallubalen da ya ke haifar wa da suka hada da talauci, rashin ilimi, rashin tsaro da rashin tarbiya."

Sanarwar ta kuma ce gwamnonin sun tuntubi Ministan Noma da Cigaban Karkara, Muhammed Sabo Nanono a kan tallafin COVID-19 da za a bai wa manoma a kasar don jin yadda yankinsu za ta amfana da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel