Da duminsa: An dakatar da gwajin Covid-19 a jihar Kano

Da duminsa: An dakatar da gwajin Covid-19 a jihar Kano

- An dakatar da gwajin kwayar cutar Covid-19 a jihar Kano sakamakon rashin kayan aikin

- Ya ce dole ne yasa suka yi hakan don babu sinadaran gwajin kwayar cutar don ci gaba da gwajin a jihar

- Amma ya ce da zarar an samar da kayayyakin gwajin, jihar Kano za ta ci gaba da aikinta

An dakatar da gwajin kwayar cutar Covid-19 a jihar Kano sakamakon rashin kayan aikin.

Farfesa Sadiq Isah na kwamitin yaki da cutar Covid-19 a Kano ya tabbatar wa da BBC hakan a ranar Laraba.

Ya ce dole ne yasa suka yi hakan don babu sinadaran gwajin kwayar cutar don ci gaba da gwajin a jihar.

Farfesan ya ce a halin yanzu, za a dinga kai samfurin da aka diba na wadanda ake zargin suna dauke da cutar har babban birnin tarayyar Abuja.

Sannan za a jira sakamakon cutar don tabbaci.

Ya ce sun sanar da hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) kuma da zarar an samar da kayayyakin gwajin, jihar Kano za ta ci gaba da aikinta.

Amma Farfesan bai bayar da tsayayyen lokacin da ake sa ran samun kayan gwajin ba.

Da duminsa: An dakatar da gwajin Covid-19 a jihar Kano
Da duminsa: An dakatar da gwajin Covid-19 a jihar Kano
Asali: UGC

KU KARANTA: Kano: 'Yan sanda sun damke limamai 15 a fadin jihar

A wani labari na daban, limamai 15 ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta damke a kan zarginsu da ake da yin sallar Juma'a ta jam'i a jihar tare da karya dokar hana zirga-zirga.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada dokar hana zirga-zirga a jihar na tsawon kwanaki bakwai. A cikin dokar kuwa, akwai haramcin taro kowanne iri har da na addinai da suka hada da sallar Juma'a da taron coci.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, DSP Haruna, wanda ya damko wadanda ake zargin a ranar Litinin, ya ce an kama su ne sakamakon zarginsu da ake yi da jan jam'in Juma'a wanda ya take dokar gwamnatin jihar.

Ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a kananan hukumomin birnin Kano, Garko, Gwale, Karaye da Tarauni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel