Kano: Bidiyon dandazon matasa na kwallo duk da doka ya jawo cece-kuce

Kano: Bidiyon dandazon matasa na kwallo duk da doka ya jawo cece-kuce

- Wani bidiyo na wasu mazauna jihar Kano ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani wanda matasa ke ta taka leda yayin dokar hana zirga-zirga

- A bidiyon, an ga matasa a jihar na karya dokar nisantar juna da gwamnatin tarayya da ta jihar suka gindaya

- Kamar yadda aka ji wanda ya nadi bidiyon yana bayyanawa, lamarin ya faru ne a anguwar Kurna da ke cikin birnin Kano

Wani bidiyo na wasu mazauna jihar Kano ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

A bidiyon, an ga matasan jihar na karya dokar nisantar juna da gwamnatin tarayya da ta jihar suka gindaya.

An ga samari cike da filin kwallo suna taka leda inda wasu daban ke zagaye dasu don kallon wasan.

Da karfe 11:10 na daren jiya Litinin ne hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta tabbatar da cewa mutum 23 ne suka sake kamuwa da cutar a jihar Kano.

Hakan ne ya kai jimillar masu cutar zuwa 59 a cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriyan.

A ranar 11 ga watan Afirilun 2020 ne jihar Kano ta tabbatar da samuwar cutar a jikin dan jihar.

Bayan kwanaki hudu wanda yayi dai-dai da 15 ga watan Afirilu, an samu mutuwar farko sakamakon cutar.

Kano: Bidiyon dandazon matasa na kwallo duk da doka ya jawo cece-kuce
Kano: Bidiyon dandazon matasa na kwallo duk da doka ya jawo cece-kuce
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga gwamnatin Najeriya

Yawan masu cutar na sake hauhawa, lamarin da yasa gwamnatin jihar ta dauka matakin hana zirga-zirga a jihar.

Amma kuma wannan bidiyon ya bayyana cewa mazauna jihar Kano basu kiyaye dokar nisantar juna don kiyaye yaduwar cutar ba.

Kamar yadda aka ji wanda ya nadi bidiyon yana bayyana, lamarin ya faru ne a anguwar Kurna da ke cikin birnin Kano.

A wani labari na daban, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje a ranar Talata ya ce jihar ta killace wasu mutane da ake zargin suna dauke da kwayar cutar coronavirus a otal domin kare yaduwar cutar a garin.

Premium Times ta ruwaito Ganduje ya ce halin da aka shiga ne ya janyo hakan yayin da ya ke jawabi ga shugaban hukumar NCDC, Chikwe Ihekweazu yayin ziyarar da ya kai Kano inji Kakakin gwamnan Abba Anwar.

Mr Anwar ya ce gwamnan ya ce, "Muna iya kokarin mu domin magance matsalar. Hakan mutane marasa karfi wadanda ake zargin suna dauke da shi ake kai su otal bayan an musu gwaji."

Ganduje ya ce dukkan wadanda aka fara gano wa suna dauke da cutar suna cikin manyan kananan hukumomi da ke cikin gari ne saboda haka an takaita yiwuwar yaduwar ta zuwa wasu unguwanni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel