Kasashe 12 masu amfani da fasahar 5G a yanzu

Kasashe 12 masu amfani da fasahar 5G a yanzu

A baya-bayan nan an yi ta zargin cewa sabuwar fasahar shiga yanar gizo ta 5G na da babbar alaka da bullar cutar coronavirus wadda ta zamto annoba a duniya.

Wannan zargi yayi tasiri da ya sanya aka rika yada wasu bidiyo a zaurukan sada zumunta da ke nuna turakun sadarwa na wayoyi na ci da wuta a garin Birmingham da Merseyside da ke Ingila.

Da yawa daga cikin masu zargin wannan kullalliya sun yi ikirarin cewa, fasahar 5G- tsarin shiga yanar gizo mai karfi shi ne ya haddasa cutar coronavirus.

Legit.ng ta fahimci cewa, an fara yada wannan zargi a shafin sadarwa na Facebook tun a karshen watan Janairu bayan bullar cutar corona karo na farko a kasar Amurka.

Kasashe 12 masu amfani da fasahar 5G a yanzu
Kasashe 12 masu amfani da fasahar 5G a yanzu
Asali: UGC

A yayin da wasu ke zargin cewa fasahar 5G na karya garkuwar jiki da hakan zai sa a kamu da cutar corona cikin sauki, wasu na ganin cewa ana amfani da fasahar ne domin a yada cutar.

Tuni masana kimiya suka yi Alla-wadai da wannan zargi, suka ce lamarin alakanta cutar corona da fasahar 5G mafi kololuwar mataki ne na wauta.

A cewar Dr Simon Clarke, Farfesa a bangaren nazarin kwayoyin halittu a Jami'ar Reading da ke Birtaniya, irin wannan tunani shirme ne kurum da masu hankali ya kamata su kauracewa.

KARANTA KUMA: Hanyoyin kaucewa rushewar Najeriya da dokar hana fita za ta haifar

Najeriya ce kasa ta farko a yankin Afirka ta Yamma da ta fara gwajin nau'rorin zamani masu amfani da fasahar 5G tun a watan Nuwamban 2019.

Sai dai rade-radin da ke yaduwa kan cewa fasahar na barazana ga lafiya ya jefa fargaba a zukatan 'yan kasar duk da ministan sadarwa, Mallam Isa Ali Pantami ya kawar da shakku.

A halin yanzu akwai kasashen duniya 12 da tun shekaru daya zuwa biyu suka fara cin moriyar sabuwar fasahar 5G, wajen shiga yanar gizo cikin sauki ba tare da bata lokaci ba.

Kasashen sun hadar da; Amurka, Australia, China, Hong Kong, Finland, Ireland, New Zealand, Norway, Philippines, Poland, Romania da kuma Thailand.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel