Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 38 sun kamu da Coronavirus a Najeriya, 23 a Kano

Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 38 sun kamu da Coronavirus a Najeriya, 23 a Kano

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane 38 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Lahadi, 19 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane talatin da takwas (38) sun kamu da #COVID19"

23 a Kano

5 a Gombe

3 a Kaduna

2 a Borno

2 a Abia

1 a Abuja

1 a Sokoto

1 a Ekiti

Kawo yanzu 11:20 na daren Litinin, mutane 665 suka kamu da cutar, 188 sun warke kuma 22 sun mutu.

Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 38 sun kamu da Coronavirus a Najeriya, 23 a Kano
Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 38 sun kamu da Coronavirus a Najeriya, 23 a Kano
Asali: Facebook

Ga jerin jihohin da adadin wadanda suka kamu:

Lagos-376

FCT-89

Kano-59

Osun-20

Oyo-16

Edo-15

Ogun-12

Kwara-9

Katsina-12

Bauchi-7

Kaduna-9

Akwa Ibom-9

Delta-4

Ekiti-4

Ondo-3

Enugu-2

Rivers-2

Niger-2

Benue-1

Anambra-1

Borno-3

Jigawa-2

Abia-2

Gombe-5

Sokoto-1

Mun kawo muku a baya cewa An samu bullar cutar Coronavirus a Sakkwaton Shehu, Gwamnatin jihar ta tabbatar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a jawabin da yayiwa manema labarai da daren Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2020.

A cewarsa, mutumin d aya kamu na kwance a asibitin koyarwan jami'ar Usamnu DanFodio, dake jihar.

Yace: "Ya ku al'ummar jihar Sokoto, cikin bakin ciki nike mai sanar muku da labaran cewa an samu bullar annobar Coronavirus a nan jihar Sokoto."

"Tunda an tabbatar da kamuwa mutumin, za'a kai shi cibiyar killacewa dake Amanawa."

"Ina kira ga al'ummar jiharmu su cigaba da biyayya ga shawarin da jami'a kiwon lafiya suka bada domin takaita yaduwar cutar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel