Garba Shehu ya mayar da martani a kan hanasu shiga Villa bayn sun halarci jana'izar Abba Kyari

Garba Shehu ya mayar da martani a kan hanasu shiga Villa bayn sun halarci jana'izar Abba Kyari

Mallam Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya mayar da martani tare da yin karin bayani a kan rahotannin cewa an wasu manya manyan hadiman Buhari shiga Villa.

A ranar Asabar ne aka hana wasu manyan hadiman shiga Villa bayan sun dawo daga jana'izar marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

A cikin jerin takaitattun sakonni da ya wallafa a shafinsa na tuwita, Garba Shehu ya ce ba wani abu ba ne don a shawarcesu su killace kansu saboda sun halarci jana'izar Abba Kyari.

"Ba wani abu bane don an ba mu umarnin nesanta kanmu daga Villa tare da ba mu shawarar mu killace kanmu bayan halartar jana'izar Abba Kyari.

"Yin hakan na daga cikin dokokin da hukumar kula da cututtuka ma su yaduwa da ma'aikatar lafiya su ka saka don dakile yaduwar annobar covid-19.

"Ma fi yawan kofofin shiga Villa na zamani ne da ke aiki da fasahar zamani wajen bawa ma su aiki a ciki damar shiga," a cewarsa.

Garba Shehu ya ce abin da ya farun ba wani sabon abu ba ne.

Dumbin mutane ne su ka halarci makabartar da aka binne Abba Kyari, yawancin mutanen basu saka takunkumin rufe fuska ko safar hannu ba a matsayin matakin kare yaduwar annobar cutar covid-19.

Akwai fargabar cewa jama'ar sun yi watsi da shawarar NCDC, lamarin da zai iya haifar da yaduwar kwayar cutar covid-19 a makabartar da jama'a su ka yi wa tsinke domin halartar binne marigayi Abba Kyari.

DUBA WANNAN: Sai an killace duk wadanda su ka taba gawar Abba Kyari - Hukumar Abuja

SaharaReporters ta ce bincikenta ya gano cewa daga cikin hadiman Buhari da aka hana shiga fadar shugaban kasa akwai; Ambasada Lawal Kazaure, Yusuf Sabiu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa.

Sauran sun hada da Musa Haro Daura, dan uwan shugaba Buhari, da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, Babagana Monguno, mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro (NSA), da sauransu.

SaharaReporters ta ce an hana manyan hadiman shiga fadar shugaban kasa ne saboda yadda su ka yi watsi da umarnin nesanta da kare kai daga kamuwa da yada cutar covid-19 yayin jana'izar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel