Ba duka 'yan Najeriya ne za a bai wa hasken lantarki kyauta ba - Gwamnati

Ba duka 'yan Najeriya ne za a bai wa hasken lantarki kyauta ba - Gwamnati

Kusoshin gwamnati a Najeriya sun fara tumke damarar rarraba hasken lantarki ga 'yan kasar kyauta har na tsawon watanni biyu.

Gwamnatin kasar ta kudiri aniyyar hakan ne domin saukakawa al'umma matsin rayuwa da za su fuskanta a yayin da annobar coronavirus ta yi sanadiyar a tilastawa 'yan kasar zaman gida.

A yunkurin haka gwamnati tare da sauran masu ruwa da tsaki ta gudanar da wani taro dangane da yadda za a bullowa lamarin na tabbatar da an wadata al'umma da hasken lantarki.

Wakilai daga majalisar tarayya da kuma masu ruwa da tsaki a fannin lantarki sun gudanar da taron ne a ranar Alhamis.

Sai dai fa gwamnatin ta ce ba dukkanin 'yan kasar ba ne za su samu hasken lantarkin kyauta domin kuwa tun a yanzu, ta bijiro da hanyoyin zakulo wadanda za su ci moriyar kudirin.

Ministan Lantarki; Saleh Mamman
Ministan Lantarki; Saleh Mamman
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnati ta bayar da sahalewarta a kan biyan N200bn domin bunkasa samuwar makamashi na iskar gas ga kamfanoni masu rarraba hasken lantarki.

Gwamnati ta malalo wannan makudan kudi domin bunkasa samun wutar lantarki a kasar yayin da annobar covid-19 ta dugunzuma dukkanin kasashen duniya.

Shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC, Mallam Mele Kyari, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba.

Shaidar Mallam Kyari ta zo ne bayan ganawarsa da ministan lantarki, Engr. Saleh Mamman da kuma shugaban kamfanin raba wutar lantarki na kasa, Usman Muhammad, a birnin Abuja.

Ya ce gwamnati ta biya fiye da Naira biliyan 200 cikin kwanaki biyu zuwa uku domin tabbatar da an samu wadatacciyar wutar lantarki a kasa baki daya.

Kyari ya ce an gudanar da zaman tattauna wannan lamari tare da ministan lantarki domin bunkasa samar da makamashin gas ga kamfanoni masu dakon wuta a kasar.

KARANTA KUMA: Covid-19: Nau'ikan abinci masu bunkasa garkuwar jiki

Ya sha alwashin kai ziyara wasu daga cikin kamfanonin rarraba wutar lantarki a yau Alhamis, domin tabbatar da 'yan Najeriya sun samu wuta a wannan lokaci da aka tilasta zaman gida.

Sauran 'yan majalisar tarayyar a yayin halarci taron sun hadar da; Alhassan Doguwa, Muhammad Monguno, Peter Akpatason, Nkeiruka Onyejeocha, Ndudi Elumelu, Magaji Da'u Aliyu da sauransu.

Tun a makonnin suka shude, an yi rade-radin cewa, kamfanonin samar da hasken lantarki sun nemi hadin gwiwar gwamnati domin bayar da wutar lantarkin ta watanni biyu kyauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel