COVID-19: Majinyaci da jami'in NSCDC sun ba hammata iska a cibiyar killacewa ta Kaduna

COVID-19: Majinyaci da jami'in NSCDC sun ba hammata iska a cibiyar killacewa ta Kaduna

- Wani mutum mai fama da cutar coronavirus sun ba hammata iska tare da wani jami'in NSCDC a cibiyar killace masu cutukan da ke yaduwa ta Kaduna

- Majinyacin wanda aka sakaya sunansa, ya hari Joshua Philip ne bayan yana gadin cibiyar kuma ya hana shi fita da zummar zai sha iska daga waje

- Tuni dai aka saka wa mabudin sinadaran kashe kwayoyin cuta sannan aka bai wa jami'in wasu magunguna, an umarceshi da ya killace kanshi na sati biyu

Wani mutum mai fama da cutar coronavirus sun ba hammata iska tare da wani jami'in NSCDC a cibiyar killace masu cutukan da ke yaduwa ta Kaduna.

Damben ya biyo bayan hana majinyacin tserewa da jami'in NSCDC din yayi daga cibiyar.

Majinyacin wanda aka sakaya sunansa, ya hari Joshua Philip ne yayin da yake gadin cibiyar kuma ya hana shi fita da zummar zai sha iska daga waje.

Kamar yadda takardar da mataimaki na musamman ga shugaban NSCDC din a fannin yada labarai, Ekuna Gbenga ya fitar, an kara tsananta tsaro a farfajiyar cibiyar don gujewa sake faruwar lamarin.

Takardar ta ce,"Wani mai fama da cutar coronavirus ya yi yunkurin tserewa daga cibiyar killacewa ta Kaduna.

COVID-19: Majinyaci da jami'in NSCDC sun ba hammata iska a cibiyar killacewa ta Kaduna

COVID-19: Majinyaci da jami'in NSCDC sun ba hammata iska a cibiyar killacewa ta Kaduna
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Ministan FCT ya sanar da kwanakin bude kasuwanni

"An ba hammata iska tsakaninsa da jami'in hukumar NSCDC bayan majinyacin yayi yunkurin amfani da karfi wajen kwatar makullin kofar don ficewa.

"Majinyacin kuwa ya dage wajen dambe da jami'in bayan ya hana shi fita daga cibiyar. Wannan lamarin kuwa yasa aka killace jami'in.

"Tuni dai aka saka wa mabudin sinadaran kashe kwayoyin cuta sannan aka bai wa jami'in wasu magunguna. An umarceshi da ya killace kansa na makonni biyu sannan ya kira cibiyar idan ya ga wata alamar cutar.

"A halin yanzu dai an kara inganta tsaro a cibiyar killacewar don gudun sake aukuwar lamarin."

A wani labari na daban, an ji cewa wani mai dauke da cutar coronavirus ya mannawa ma'aikaciyar jinya mugun cizo a hannunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel