Yanzu-yanzu: An sallami mutane 5 a Legas, 4 a Bauchi bayan samun waraka daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 5 a Legas, 4 a Bauchi bayan samun waraka daga Coronavirus

An samu karin mutane 9 masu cuta mai toshe numfashi watau Coronavirus da suka samu sauki da lafiya bayan kwashe kwanaki suna jinya a jihar Legas da Bauchi.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita a ranar Alhamis.

Ya ce an sallamesu ne bayan gwajin karshe da akayi ya nuna cewa sun barranta daga cutar.

Yanzu haka, adadin wadanda aka sallama a Legas ya kai 85.

A jihar Bauchi kuwa, an sallami mutane hudu da suka samu sauki daga cutar bayan cika sharrudan da hukumar kula da dakile yaduwar cututtuka NCDC ta kindaya.

Mataimakin gwamnan jihar, wanda shine shugaban kwamitin yaki da annobar a jihar, Sanata Baba Tela, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis a jihar.

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 16 a Legas, 4 a Bauchi bayan samun waraka daga Coronavirus
Coronavirus
Asali: Twitter

KU KARANTA Tallafi 17 da Gwamnatin tarayya ta samu domin yaki da cutar COVID-19

A bangare guda, an samu karin mutane 5 masu cuta mai toshe numfashi watau Coronavirus da suka samu sauki da lafiya bayan kwashe kwanaki suna jinya a jihar Kwara da Akwa Ibom.

A jihar Kwara, gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa an sallami mutane biyu a jiharsa bayan gwaji biyu daban-daban sun nuna cewa sun barranta daga cutar.

Ya kara da cewa an sallamesu tare da yan uwansu da aka killace saboda ana tsoron sun kamu da cutar amma basu kamu ba.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Alhamis a Ilori, babbar birnin jihar.

Yace "Ina farin cikin sanar muku da cewa zamu sallami mutane bakwai daga cibiyar killace marasu lafiyarmu."

" Cikin akwai mutane biyu da suka fara kamuwa da cutar a jiharmu."

A jihar akwa Ibom kuwa, gwamnatin jihar ta yi farin cikin sanar da cewa an sallami mutane uku cikin biyar masu cutar Coronavirus a jihar.

Kwamishanan lafiyan jihar, Dr Dominic Ukpong, wanda yayi sanarwan ya ce an sallamesu ne bayan gwajin karshe da akayi musu ya nuna cewa sun warke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel