Tsohon dan takarar gwamna a Bayelsa ya mutu yayin tiyatar rage kitse

Tsohon dan takarar gwamna a Bayelsa ya mutu yayin tiyatar rage kitse

Keneibi Okoko, tsohon dan takarar gwamna a jihar Bayelsa, ya mutu yayin yayin wata tiyata da ake yi masa a wani asibiti mai zaman kansa a Legas.

An samu tangarda yayin tiyatar da ake kira 'liposuction', wacce masana su ka ce ana gudanar da ita ne domin rage wa mutum kitse a cinya, dantse, ciki da sauran sassan jiki.

Takardar shaidar mutuwarsa ta nuna cewa an kai shi wani asibiti mai suna 'Amethyst Health Care Diagnostic Centre Limited, domin duba yana da ya haifar da tsirowar kitse mai yawa a cikinsa da nonuwansa.

"Ya mutu ne ranar Laraba, 16 ga watan Afrilu, sakamakon shaqewar numfashi da bugun zuciya," a cewar takardar mai dauke da sa hannun wakilin asibitin, Benedict Olusola.

A ranar 10 ga watan Afrilu ne Okoko ya yi rabon tallafi ga jama'ar mazabarsa da ke Obunagha a karkashin karamar hukumar Yenagoa.

Ya bayar da tallafin ne a matsayin gudunmawarsa ga talakawa da marasa karfi yayin da aka saka dokokin kule da hana zirga - zirga a jihohi don dakile yaduwar cutar covid-19.

Tsohon dan takarar gwamna a Bayelsa ya mutu yayin tiyatar rage kitse
Tsohon dan takarar gwamna a Bayelsa ya mutu yayin tiyatar rage kitse
Asali: Twitter

Daga jihar Delta mai makwabtaka da Bayelsa, an harbi wani matashi yayin da dandazon mata da matasa su ka fito domin gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsawaita dokar hana fita a karamar hukumar Sapele.

Matashin da aka harba na daga cikin daruruwan fusatattun matasa da mata da su ka fito gudanar da zanga-zangar nema a basu tallafin jin kai tunda aka kara wa'adin sati biyu a kan dokar kulle da hana jama'a fita.

Duk da an samu rudani a kan harbin matashin, majiyar jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa daya daga cikin jami'an tsaro da suka zo domin kwantar tarzoma ne ya harbe shi.

DUBA WANNAN: Fatima Garba: Rundunar 'yan sanda ta cafke wata mata da ke safarar makamai ga masu garkuwa da mutane

Majiyar ta bayyana cewa an garzaya da matashin zuwa wani asibiti domin ceton ransa.

"Jami'an tsaro sun zo wurin domin tarwatsa ma su zanga - zangar. Ina jin a kokarin tarwatsa jama'ar ne su ka harbi matashin a kugu," a cewar majiyar, wacce ta nemi a boye sunanta.

Yayin zanga - zangar, fusattaun matasan sun dinga rera wakar "a bamu abinci, "ba zamu saurari duk wani zance ba".

A ranar Talata ne gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya fitar da sanarwar kara sati biyu a kan dokar hana fita daga gida da taron jama'a biyo bayan karewar wa'adin sati biyun farko da ya ayyana.

An harbi mutum daya yayin da mata da matasa su ka fito zanga-zangar hana fita a Delta

Da ya ke rokon jama'a a kan su bi umarnin hukuma da yin biyayya ga dokokin da ta gindaya, Okowa ya ce karin satin biyun za su taimaka wajen zakulo wadanda suka yi mu'amala da mutane uku da aka tabbatar su na dauke da cutar covid-19 a jihar.

Kazalika, gwamnan ya bawa jama'ar jihar tabbacin cewa za a raba musu kayan abinci zuwa karshen makon da mu ke ciki.

Amma, fusattatun ma su zanga - zangar sun bayyana cewa mugunta ce ta sa gwamnati ta kara tsawon wa'adin dokar zama a gida bayan ba su da wutar lantarki da abinci a gidajensu.

Masu zanga - zangar da yawancinsu ke sanye cikin jajayen kaya, sun bayyana cewa gwamnati ba ta damu ko yunwa za ta kashesu a gidajensu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel