Borno: Gobara ta lashe gidaje 700 a sansanin 'yan gudun hijira

Borno: Gobara ta lashe gidaje 700 a sansanin 'yan gudun hijira

A kalla gidaje 700 ne suka lalace a yayin da gobarar da ta tashi a sansanin yan gudun hijira da ke karamar hukumar Mafa na jihar Borno.

Sakataren gundunmar, Mohammed Lawan Sharrif ne ya bayyana hakan yayin hirar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, a ranar Talata a Maiduguri.

Mista Lawan Sheriff ya ce gobarar da ta fara ci tun karfe 11 na safiyar ranar Talata ta kuma dauki awanni tana ci ta kone gidaje da dama a sansanin.

Ya ce gobarar da ta fara daga gida guda daya ta yadu zuwa sauran gidajen saboda babu jamian hukumar kashe gobara a lokacin da lamarin ya faru.

Borno: Gobara ta lashe gidaje 700 a sansanin yan gudun hijira
Borno: Gobara ta lashe gidaje 700 a sansanin yan gudun hijira
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade

Ya ce sauran mazauna sansanin gudun hijirar, jamian sa kai na Civilian JTF, jamian tsaro da sauran alumma ne suka taimaka aka kashe gobarar.

Ya ce, "Muna jin cewa gobarar ta tashi, mun tattara mutane daga unguwar da sansanin ya ke domin zuwa wurin da gobarar ta tashi domin a kashe ta. Kawo yanzu babu wanda ya mutu."

Sakataren ya ce ofishinsa da sauran abokan hulda suna aiki tare domin ganin sun tallafawa wadanda abin ya shafa da kayan masarufi da wasu abinda za su bukata na yau da kulum.

Ya ce, "Mun umurci manajojin sansanin guda 11 su yi nazarin abinda aka yi asara kuma su kirga mutanen da ke sansanin domin tabbatar da cewa kowa yana nan lafiya kuma an kawo motar daukan marasa lafiya."

Akwai mutane 4,782 a sansanin gudun hijirar na Mafa galibinsu mata ne da yara da kuma tsofaffi kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel