COVID-19: Ganduje ya bada umarnin garkame jihar Kano na sati daya

COVID-19: Ganduje ya bada umarnin garkame jihar Kano na sati daya

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bada umarnin garkame jihar na mako daya

- Dokar hana shige da ficen za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2020

- Gwamnan ya tabbatar da cewa jami'an tsaro za su damke duk wanda aka kama da laifin take dokar

Mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe jihar na mako daya.

Dokar hana shige da fice a jihar Kano din za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2020.

Kamar yadda mai bada shawara ta musamman ga gwamnan ya wallafa, ana sa ran dokar hana shige da ficen za ta yi aiki ne mako daya cif kafin a ga abinda hali yayi.

A tsawon lokacin, ba a bukatar kaiwa da kawowar jama'a ko ababen hawa a jihar. Gwamnan ya tabbatar da cewa jami'an tsaro za su damke duk wanda aka kama da laifin take dokar.

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamnatin Kano za ta rufe wasu kasuwannin jihar

Wannan dokar ta biyo bayan samun mutane hudu masu dauke da cutar coronavirus da aka yi a jihar Kano.

A wani labari na daban, Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje ta ce za ta rufe wasu daga cikin kasuwannin da ke jihar tare da tsananta dokar hana shiga da fice a kan iyakokinta.

Hakan kuwa ya faru ne sakamakon bullar muguwar cutar coronavirus a jihar a ranar Asabar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya shaidawa BBC cewa tuni aka killace wanda aka samu da cutar a asibitin Pfizer na kwanar Dawaki.

Dan shekaru 75 din da haihuwa na nan a killace don hana yaduwar cutar a jihar.

Ganduje ya ce, ya zama dole gwamnatin jihar ta dauki matakai masu tsanani don hana cinkoson jama'a duk da hakan zai iya takura al'ummar jahar.

A halin yanzu, jihar Kano ta zama cikin jihohin Arewa da aka samu bullar muguwar cutar tun bayan bullar cutar a jihohin Kaduna da Katsina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel