Gwamnatin jihar Katsina a umurci ma'aikatanta su koma bakin aiki

Gwamnatin jihar Katsina a umurci ma'aikatanta su koma bakin aiki

Gwamnatin jihar Katsina, karkashin gwamna Aminu Bello Masari, ta umurci dukkan ma'aikatan jihar su koma bakin aiki daga karfe 10 na safe zuwa karfe 2 na kowace rana.

A jawabin da shugaban ma'aikatan jihar, Idris Usman Tune, ya saki, ya ce gwamnan jihar ne ya bada umurnin hakan.

Idris Tune ya bukaci ma'aikatan gwamnatin su cigaba da zuwa aiki domin amsa bukatun mutane.

Ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar na iyakan kokarinta wajen ganin cewa ta takaita yaduwar cutar ta Coronavirus a jihar.

Saboda haka, shugaban ma'aikatan ya yi kira ga ma'aikatan su rika baiwa juna tazara, su rika wanke hannayensu duk inda suke, kuma su rika amfani da ruwan sanitizer.

Gwamnatin jihar Katsina a umurci ma'aikatanta su koma bakin aiki
Gwamnatin jihar Katsina a umurci ma'aikatanta su koma bakin aiki
Asali: Twitter

KU KARANTA Yayi wuf! Kansilan da aka baiwa kayan abinci ya rabawa mutane ya bace bat

A makon da ya gabata mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin jihar Katsina ta janye dokar dakatad da Sallar Juma'a a jihar bayan ganawar shugabannin addini, sarakunan gargajiya da jami'an tsaro a jhar.

Hakan ya biyo bayan mutuwar wani Likita mazaunin garin Daura, Dakta Aliyu Yakubu, sakamakon cutar a makon nan.

Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, a jawabin da ya saki ranar Laraba ya ce an janye dokar dakatad da Sallolin Juma'a amma akwai sharruda da aka kindaya na kiwon lafiya da tsaro.

A cewarsa, an shawarci Limaman Juma'a su takaita hudubobinsu domin sallamar Masallatai cikin kankanin lokaci.

Wannan matakin ya biyo bayan abinda ya faru ranar 28 ga Maris, inda daruruwan matasa suka ci karo da 'yan sanda a karamar hukumar Kusada da ke jihar Katsina a kan damke wani limamin garin da aka yi.

'Yan sandan sun kama limamin sakamakon karantsaye da yayi ga dokar gwamnatin jihar da ta hana kowanne taron addinin a matsayin hanyar hana yaduwar muguwar cutar coronavirus.

Majiya mai karfi ta bayyana cewa wasu 'yan sandan sun ziyarci gidan malamin ne mai suna Malam Hassan.

Sun bukaci tafiya da shi don amsa tambayoyi a kan dalilin da yasa ya yi jam'in, lamarin da mazauna yankin basu so ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel