Tsohon dan kwallon Manchester United, Fellaini ya warke daga cutar Coronavirus

Tsohon dan kwallon Manchester United, Fellaini ya warke daga cutar Coronavirus

An sallami tsohon dan kwallon kungiyar Manchester United, Marouane Fellaini daga asibitin kasar China inda ya yi jinya bayan kamuwa da annobar Coronavirus mai toshe numfashi.

Kungiyarsa ta Shandong Luneng da Fellaini ke bugawa kwallo ce ta bayyana haka, inda tace duk da an sallame shi, za ta killace shi na tsawon makonni biyu don tabbatar da wartsakewarsa.

KU KARANTA: Azumin bana babu Tafsiri a Masallacin Sultan Bello na Kaduna – Babban Limami

A ranar 22 ga watan Maris ne Fellaini ya bayyana kamuwa da cutar jim kadan bayan shigarsa kasar China, daga nan ne kuma aka garzaya da shi asibitin Jinan, inda ya yi jinya.

Shandong Luneng ta ce: “An duba Fellaini, kuma an tabbatar ya warke, don haka aka sallame shi a yau.” Ana sa ran Fellaini zai cigaba da taka leda da zarar an cigaba da gasar kasar China.

Tsohon dan kwallon Manchester United, Fellaini ya warke daga cutar Coronavirus
Tsohon dan kwallon Manchester United, Fellaini ya warke daga cutar Coronavirus
Asali: Facebook

Fellaini ya koma Shandong Luneng ne a watan Feburairun shekarar da ta gabata a kan kudi Yuro miliyan 7.2, kuma ya zura kwallaye 12 a wasanni 34, tare da bayar da kwallaye 5.

A wani labarin kuma, Tun bayan bullar annobar Coronavirus, an samu sauye sauye da dama a al’amuran duniya gaba daya, wanda ya sauya salon tafiyar da hidindimu da yawa

A nan gida Najeriya ma wannan annoba ta kawo sanadiyyar sauya salon tafiya da al’amura, tun daga kulle makarantu, kulle kasuwanni, wuraren ibada da ma karya tattalin arziki.

Wannan tasa kwamitin Masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna ta yanke shawarar dakatar da gudanar da tafsirin Al-Qur’ani mai girma kamar yadda aka saba yi a cikin Masallacin.

Fitaccen Malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi ne yake gudanar da tafsiri a Masallacin a duk lokacin azumin watan Ramadana, amma an samu sauyi a azumin bana saboda COVID-19.

Babban limamin Masallacin, Farfesa Muhammad Sulaiman Adam ne ya bayyana haka, inda yace a bana Malam Ahmad Gumi zai gudanar da tafsirin ne daga wani wuri na daban.

Sulaiman yace Malam Gumi ne kadai zai gudanar da Tafsirin tare da majabakinsa, kuma za’a watsa karatun a kafafen sadarwa na gani da na saurare, da shafukan sadarwar zamani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel