Coronavirus: Babu Sallar Tarawihi bana - Kasar Saudiyya ta bayyana

Coronavirus: Babu Sallar Tarawihi bana - Kasar Saudiyya ta bayyana

Ma’aikatar lamuran addinin Musulunci, Da’awah, da shiryar da a’umma na Saudiyya ta bayyana cewa mutane su shirya gudanar da Sallar Tarawihi a gidajensu saboda ba za'a bude Masallatai ba.

Sallar Tarawihi wacce aka fi sani da Sallar Asham, wasu raka’o’i ne da ake gudanarwa bayan Sallan Isha’i a cikin watar Ramadana.

Gwamnatin Saudiyya ta ce sam ba zata daga dokar rufe Masallatai ba sai cutar Coronavirus ta kare gaba daya.

Jaridar Al-Riyadh ta ruwaito Ministan lamuran addinin Musulunci, Dr. Abdul Latif Al Sheikh, da cewa Sallolin farilla biyar da aka dakatar sun fi Tarawihi muhimmanci.

Yace: “Dakatad da Sallolin Khamsu-Salawati a Masallatai ya fi muhimmanci da dakatad da Sallar Asham. Muna rokon Allah ya karbi Sallolin Tarawihin ko da an yi a Masallatai ko gidaje, kuma hakan ya fi kyau ga lafiyar mutane.“

“Muna rokon Allah ya karbi adduoinmu kuma ya kare duniya daga annobar da ta addabi al“ummar duniya.“

Coronavirus: Babu Sallar Tarawihi bana - Kasar Saudiyya ta bayyana
Coronavirus: Babu Sallar Tarawihi bana - Kasar Saudiyya ta bayyana
Asali: Facebook

A bangare guda, Gwamnatin kasar Saudiyya ta kindaya wasu ka'idoji ga iyalan dukkan wanda ya mutu sakamakon cutar Coronavirus saboda hana yaduwar cutar.

Masana kiwon lafiya da ilmin kwayoyin cututtuka sun bayyana cewa ana iya kamuwa da cutar ta Coronavirus daga jikin mutumin da ya mutu sakamakon cutar.

Haka ya sa an daina yiwa gawawwakin Musulmai wanka Jana'iza da ruwa; sai Taimama.

Ma'aikatar kiwon lafiyan kasa tace mutane biyar zuwa shida daga iyalan mamaci ne aka amince su gudanar da Sallar Jana'iza.

Yayinda ministan lamuran addinin Musulunci, Da’awah, da shiryar da a’umma na Saudiyya, Dr. Abdul Latif Al Sheikh, yake tsokaci kan hakan, ya ce Sallar Jana'iza bata kai na farilla muhimmanci ba.

Yace taruwar mutane a waje na iya rura yaduwar cutar cikin al“umma.

Yace “Wannan mataki ne da aka dauka na haramta taro na cewa a yi Sallolin Jana'iza a makabartu kuma kada iyalan mamacin sun wuce biyar ko shiga, sauran suyi sallarsu a gida.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel