Mun mayarwa direban da dan sanda ya kwacewa N40,000 kudinsa - Hukuma

Mun mayarwa direban da dan sanda ya kwacewa N40,000 kudinsa - Hukuma

- Daga karshe, Direban da dan sanda ya kwacewa kudi ya samu kudinsa

- Hukumar yan sanda ta daura hoton mutumin a Tuwita yayinda ake mika masa kudinsa

- An damke dan sandan da ya aikata wannan abin kunyan

Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta mayarwa direban da daya daga cikin jami'anta ya kwacewa kudi N40,000 dan ya hau titi lokacin dokar hana fita a jihar Legas.

Kaakin hukumar yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya bayyana hakan ranar Lahadi a wani jawabi inda ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya mayar masa da kudin.

KU KARANTA Coronavirus An sallami 15 amma an samu karin mutane 5 da suka kamu a Najeriya

Mun mayarwa direban da dan sanda ya kwacewa N40,000 kudinsa - Hukuma

Mun mayarwa direban da dan sanda ya kwacewa N40,000 kudinsa - Hukuma
Source: Facebook

Mun kawo muku rahoton wani dan sanda da ke aiki a Okota da ke Oshodi, karamar hukumar Isolo da ke jihar Legas ya shiga hannun hukuma bayan an gano ya karba cin hanci daga masu ababen hawa.

An ga wani dan sanda mai matsayin sifeta mai suna Taloju Martins yana kirga takardun dubu daddaya har guda arba'in a wani bidiyo.

Kudin dai tamkar na fansa ne wanda wani mai abun hawa ya bashi don ya sakar masa abun hawansa.

Ya zargin mai abun hawan da karya dokar kullen da gwamnatin jihar ta saka don hana yaduwar muguwar cutar coronavirus a jihar ta Legas.

Dan sandan ya bukaci mai abun hawan da aka kwacewa mota da ya biya N50,000 amma sai ya roka aka bar mishi a N40,000.

Amma kuma a rashin sanin Martins, mai motar ya nadi bidiyonsa a yayin da suke yin wannan cinikin.

Kamar yadda bidiyon da mawaki mai suna Rugged Baba ya wallafa, ya ce lamarin ya faru a ranar Juma'a ne, 10 ga watan Afirilu a titin fadar Ago da ke Okota.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel