Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 13, Jimilla 318

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 13, Jimilla 318

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane goma sha uku (13) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Asabar, 11 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane goma sha uku (13) sun kamu da #COVID19; 11 a Lagos, 1 a Delta & 1 a Kano.“

“A karfe 9:30 na daren 11 ga Afrilu, mutane 318 suka kamu da COVID19 a Najeriya. 70 sun warke, kuma 10 sun mutu.“

“An tabbatar da bullar cutar a jihohi 19 a Najeriya.“

Ga jerin:

Lagos- 174

FCT- 56

Osun- 20

Edo- 12

Oyo- 11

Ogun- 7

Bauchi- 6

Kaduna- 6

Akwa Ibom- 5

Katsina-4

Delta- 3

Enugu- 2

Ekiti- 2

Rivers-2

Kwara- 2

Ondo- 2

Benue- 1

Niger- 1

Anambra- 1

Kano-1

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 13, Jimilla 319
Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 13, Jimilla 319
Asali: UGC

A wani labarin daban, Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanar da rufe gaba daya harkoki a jahar daga ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu.

Hakan na zuwa ne bayan an gano mutum na farko da ke dauke da cutar COVID-19 wacce aka fi sani da coronavirus a jahar.

A cewar kwamishinan lafiya na jahar, Dr. Muhammad Maikusidi, lamarin ya fito ne daga yankin Limawa a Minna, babbar birnin jahar.

Gwamnan ya umurci tawagar COVID-19 na jahar da su killace yankin na tsawon kwanaki 14.

Gwamnan ya kuma yi umurnin ci gaba da dakatar da dukkanin harkoki na addini har sai baba ya gani.

KU KARANTA Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel