Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 16, Jimilla 305
Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane goma sha bakwai (17) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Jumaa, 10 ga Afrilu, 2020.
Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma sha shida(16) sun kamu da #COVID19 a Najerya,
8 a Lagos
3 a Katsina
2 a Abuja
1 a Neja
1 a Kaduna
1 a Anambra
1 a Ondo
“Kawo karfe 9:30 na yammacin 10 ga Afrilu, mutane 305 aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya, an sallami mutane 58, kuma mutane 7 a rigamu gidan gaskiya.“

Asali: Facebook
A yau, Juma'a, ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da kwamitin 'ko ta kwana' da ya kafa a kan annobar cutar covid-19.
A cikin wata sanarwa da shugaba Buhari da kansa ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa ya na matukar godiya ga kwamitin bisa jajircewarsa a kan aikin da aka dora masa.
Kazalika, ya nuna karfin gwuiwarsa a kan cewa kokarin da kwamitin ya ke yi, zai bawa Najeriya damar samun nasara a kan wannan annoba.
"A yau ne kwamitin ko ta kwana a kan shawo kan annobar cutar covid-19 ya kawo min ziyara domin yi min bayani a kan aiyukansu da halin da ake ciki.
"Ina mai farin ciki da godiya bisa jajircewarsu wajen sauke nauyin da aka dora musu. Ba ni da kokonto ko kadan a kan cewa kokarinsu zai bawa Najeriya damar samun nasara a kan annobar," a cewar Buhari.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng