Buhari ya gana da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 (Hotuna)

Buhari ya gana da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 (Hotuna)

A yau, Juma'a, ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da kwamitin 'ko ta kwana' da ya kafa a kan annobar cutar covid-19.

A cikin wata sanarwa da shugaba Buhari da kansa ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa ya na matukar godiya ga kwamitin bisa jajircewarsa a kan aikin da aka dora masa.

Kazalika, ya nuna karfin gwuiwarsa a kan cewa kokarin da kwamitin ya ke yi, zai bawa Najeriya damar samun nasara a kan wannan annoba.

"A yau ne kwamitin ko ta kwana a kan shawo kan annobar cutar covid-19 ya kawo min ziyara domin yi min bayani a kan aiyukansu da halin da ake ciki.

"Ina mai farin ciki da godiya bisa jajircewarsu wajen sauke nauyin da aka dora musu. Ba ni da kokonto ko kadan a kan cewa kokarinsu zai bawa Najeriya damar samun nasara a kan annobar," a cewar Buhari.

Shugaba Buhari ne ya kafa kwamitin na 'ko ta kwana' a karkashin jagorancin ministan lafiya, Dakta Osagie Enahire, bayan bullowar annobar cutar covid-19.

A wani labarin mai nasaba da annobar covid-19, Legit.ng ta wallafa cewa, gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarnin rufe karamar hukumar Daura; ba shiga, ba fita, bayan an tabbatar da samun mutane uku da suke dauke da kwayar cutar covid-19.

Sanarwar rufe jihar ta fito ne a yau, Juma'a, kamar yadda jaridu da dama a fadin kasa suka wallafa.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ne ya bayar da umarnin rufe karamar hukumar bayan an tabbatar da bullar annobar covid-19 a yankin.

Buhari ya gana da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 (Hotuna)
Buhari yayin gana wa da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 a fadarsa
Asali: Twitter

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, dan asalin karamar hukumar Daura ne.

A jerin wasu sakonni da aka wallafa a shafin Tuwita, Masari ya ce an tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin mata da 'ya'yan likitan da kwayar cutar covid-19 ta kashe a Katsina a cikin satin nan.

Masari ya bayyana cewa an tura jinin mutane 23 domin gudanar da gwaji a kansu bayan mutuwar likitan, kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa matarsa da 'ya'yansa sun kamu da kwayar cutar.

DUBA WANNAN: NSIP: Hadimar Buhari ta mayarwa da Lawan da Gbajabiamila martani a kan sukar shirin bayar da tallafi

Gwamnan ya ce, gwamnati za ta bayar da tallafi ga mazauna karamar hukumar na tsawon lokacin da dokar za ta cigaba da aiki.

"Za mu cigaba da sa ido da bibiyar al'amura. Ba za mu yi kasa a gwuiwa ba wajen saka dokar rufe duk wata karamar hukuma da aka tabbatar da samun bullar annobar covid-19 ba. Ita kanta jihar za mu iya rufeta gaba daya idan yanayi ya nuna akwai bukatar yin hakan.

"Za mu bar shagunan sayen magani da na kayan abinci guda uku, wadanda jama'a za su ke sayen kaya a wurinsu bisa sa idon hukuma domin tabbatar da biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar cutar," a cewar Masari.

Buhari ya gana da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 (Hotuna)
Buhari yayin gana wa da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19
Asali: Twitter

Buhari ya gana da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 (Hotuna)
Buhari ya na gana wa da mambobin kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19
Asali: Twitter

Buhari ya gana da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 (Hotuna)
Buhari da mambobin kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19
Asali: Twitter

Buhari ya gana da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 (Hotuna)
Buhari da ministan lafiya
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel