Maganin COVID19: Ku gwada amfani da Habbatus-Saudi da Zuma - Sarkin Musulmi Ga WHO

Maganin COVID19: Ku gwada amfani da Habbatus-Saudi da Zuma - Sarkin Musulmi Ga WHO

- Bayan kwanaki 100 da bullowarcutar Coronavirus a duniya, har yanzu ba a gano maganinta ba

- Masana ilmin kwayoyin cuta a fadin duniya na iyakan kokarinsu wajen samo ko da rigakafi ne

- Sarkin Musulmi ya yi imanin cewa Zuma da Habbatus zasu warkar da cutar da yardan Allah

Yayinda duniya ke cigaba da laluben maganin cutar Coronavirus bayan kwanaki 100 da bullowarta, Mai alfarma sarkin Musulmi ya baiwa kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO satar amsa.

Sarkin Musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta sharia NSCIA, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce a yi dubi cikin Zuma da Habbatus Sauda saboda hadisan Manzon Allah (SAW).

A jawabin da Alhaji Yusuf Nwoha, mataimakin shugaban NSCIA ya saki, ya ce daya daga cikin magungunan da manzon Allah yayi amfani da su sune Zuma da man Habbatus-Sauda.

Daya daga cikin hadisan riwayar Abu Hurayrah inda manzon Allah yace: “Kuyi amfani da Habbatus Sauda saboda ko shakka babu tana warkar da duka cututtuka illa mutuwa.“

A wani Hadisin kamar yadda yazo a Sahihul Bukhari, manzon Allah (SAW) yace: “Zuma na maganin ko wani cuta kuma Al-Kur’ani na maganin dukkan cututtukan zuciya. Saboda haka ina baku shawara kuyi amfani dasu, Qur’ani da Zuma.”

KU KARANTA An kafa cibiyar gwajin Coronavirus a Kano, ta farko a Arewacin Najeriya

Sultan ya cigaba da cewa ”Zuma, da kanta, tana da karfin kashe kwayar cututtukan da ba a iya gani, kara karfin garkuwar jiki, taimkawa wajen saurin warkewar ciwo, warkar da ciwon ciki, gyambon ciki, Dss.”

Wannan ya biyo bayan shaidar alheri da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, yayi bayan samun waraka daga cutar Coronavirus.

Yace: “Abokina kuma dan’uwa shugaban hukumar kananan asibitocin jihar Oyo, Dakta Muyideen Olatunji, ya kira ya ce min , kai, bari in aiko maka da man habbatus sauda, tana kara karfin garkuwar jiki.”

”Sai na hada da Zuma ina shan cokali daya a safe da yamma. Saboda haka akwai magungunan gargajiya na kara karfin garkuwan jiki. Mutane su daina tsoro.”

”Kamar yadda na samu karfin korar cutar daga jikina, yawancin mutane za su iya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel