Idan mutum ya warke daga Coronavirus ba zai sake iya kamuwa da cutar ba - Masani ilmin kwayoyin cuta

Idan mutum ya warke daga Coronavirus ba zai sake iya kamuwa da cutar ba - Masani ilmin kwayoyin cuta

Wani Malami kuma masanin ilmin kwayoyin cuta, Farfesa Sunday Omilabi, ya bayyana cewa duk wanda ya samu warkewa daga cutar Coronavirus ya samu wani irin garkuwar jiki mai karfi.

Wannan garkuwa jiki za ta kareshi daga iya sake kamu da cutar a nan gaba.

Farfesa Omilabu, wanda ma'aikaci ne a asibitin koyarwan jami'ar Legas, Idi Araba, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a hirar da yayi da mambobin kungiyar marubuta labaran kiwon lafiya a Najeriya wato Health Writers’ Association of Nigeria (HEWAN).

A cewarsa, idan mutum ya warke daga cutar, hakan na nufin cewa ya samu wasu sabbin garkuwan jiki isassu.

Idan mutum ya warke daga Coronavirus ba zai sake iya kamuwa da cutar ba - Masani ilmin kwayoyin cuta
Idan mutum ya warke daga Coronavirus ba zai sake iya kamuwa da cutar ba - Masani ilmin kwayoyin cuta
Asali: UGC

KU KARANTA NCDC ta karyata batun kashe N1bn don aikewa yan Najeriya da sakonnin waya

Yace “Har yanzu bamu samu labarin wanda ya warke da ya sake kamuwa da cutar ba ko wani sashen jikinsa ya lalace ba.“

“Kuma ban tunanin akwai wani nakasa da mutum zai samu saboda muddin mutum ya tsira daga COVID-19, zai kara karfi.“

“Ana kyautata zaton cewa mutum kara samu garkuwan jiki masu karfi.“

“Yawancin wadanda aka sallama daga asibiti sun yi gwaji akalla sau biyu wanda ya nuna cewa sun warke kuma yawunsu bai dauke da kwayar cutar ko daya.“

“Saboda haka babu wani tsoron mutum zai iya sake kamuwa, amma muna bukatar karin bincike kafin iya yanke haka.“

Farfesa Omilabu ya yi kira ga yan Najeriya su tsafta tare da baiwa juna tazara domin taimakawa gwamnati wajen yakar cutar Coronavirus.

A bangare guda, Olorunnimbe Mamora, karamin ministan lafiya na kasar nan yace bai san abinda ya warkar da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ba daga cutar coronavirus da ta kama shi.

A ranar Laraba ne Mamora ya bayyana hakan ga kwamiti na musamman na shugaban kasa a kan cutar, a babban birnin tarayyar Abuja.

Mamora ya ce, "Ban san yadda aka yi mai girma gwamnan jihar Oyo ya warke daga cutar coronavirus ba".

Ya ci gaba da cewa, "Ban san a asibitin da aka kaishi har ya karba magani ba. Zan so in samu bayanan don in fitar da takardar".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel