Za mu fara kama masu yaudarar mutane da maganin coronavirus na bogi - Magu

Za mu fara kama masu yaudarar mutane da maganin coronavirus na bogi - Magu

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin kasa zagon kasa, EFCC ta ja kunnen jama'a a kan yadda wasu 'yan damfara ke tallata magungunan muguwar cutar coronavirus.

Mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya fitar da wannan takardar ne wacce Tony Orilade, mukaddashin kakakin hukumar yasa hannu.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Magu ya ce akwai bukatar 'yan Najeriya masu kishin kasa da su kiyaye wa masu gwaji da masu bada tallafin bogi ga jama'a.

Magu ya ja kunnen jama'a masu amfani da manhajoji wadanda ba amintattu ba da su kiyaye.

COVID-19: Za mu fara kama wadanda ke yaudarar mutane da magungunan karya - Magu
COVID-19: Za mu fara kama wadanda ke yaudarar mutane da magungunan karya - Magu
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An sako shahararren dan wasan kwallon kafa Ronaldinho daga gidan yari

Shugaban EFCC din yace, "Gwamnatin tarayya ta bayyana bayanan bankunan da ta amince a tura gudumawa. Duk wani bayanin da ya ci karo da hakan na damfara ne kuma abin gudu".

Ya kara da cewa, "Ya kamata jama'a su gano damfara a wuraren saka hannayen jari na yanar gizo wadanda suka hada da masu ninka kudi. Muna bibiyar irinsu kuma za mu kama su da masu daukar nauyinsu".

Kamar yadda takardar ta bayyana, shugaban EFCC din ya jawo hankalin 'yan Najeriya a kan "Robo Calls".

Kamar yadda yace, wadannan kiran ana yinsu ne don damfara tare da kwashe bayanan asusun bankin mutum.

Ya ce, "Kada ku latsa komai idan aka kiraku ta Robo. A kan bukaci a latsa wasu lambobi. Wannan damfara ce".

Magu ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa EFCC na sane da duk 'yan damfara da ke habaka harkokinsu sakamakon barkewar annobar coronavirus.

Ya ce hukumar za ta fallasa tare da damke duk wasu cibiyoyi da aka shirya don damfarar gumin 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel