COVID-19: Buhari zai fara yi wa fursunoni afuwa na musamman a ranar Alhamis
A gobe Alhamis 9 ga watan Maris ne gwamnatin tarayya za ta fara sakin fursunonin da shugaban kasa ya yi wa afuwa ta musamman a yunkurin ta na rage cinkoso a gidajen na gyaran hali.
Leadershi ta gano cewa za a fara sakin fursunonin ne bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da bukatar da ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya gabatar masa don rake cinkoso a gidajen yarin.
Gwamnatin tarayyar ta Najeriya ta dauki wannan matakin ne domin rage yaduwar cutar coronavirus a kasar.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: Coronavirus: Dole 'yan Najeriya su yi watsi da addini - Guru Maharaj Ji
Wannan sakon na cikin wata takardar gayyata ta musamman ne da ofishin ministan ya aike wa manema labarai na gayyatarsu taro a hedkwatan hukumar kula da gidajen gyaran hali na kasa (NCoS.
Mai magana da yawun hukumar da NCoS, DCC A.C. Njoku ne ya saka hannu a kan sakon.
Ministan zai jagorancin wata tawaga ta musamman zuwa gida gyaran hali na Kuje da ke Abuja domin kaddamar da shirin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng