Yanzu-yanzu: Ofishin Akawunta Janar na tarayya ta kama da wuta (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Ofishin Akawunta Janar na tarayya ta kama da wuta (Hotuna)

Ofishin akawunta janar na tarayya na ci bal-bal yanzu haka.

Ginin da aka fi sani da 'Gidan baitul mali' wato Treasury House' na kusa da hedkwatar hukumar yan sandan Abuja, a unguwar Garki.

Har yanzu ba a san abinda ya sabbaba gobarar ba duk da cewa ma'aikata na gida sakamakon dokar hana fita.

Amma jami'an kwana-kwana da wasu jami'an tsaro sun fara kashe wutar kuma sun shawo kanta.

Kalli bidiyoyin

Karamin ministan kasafi da tsare - tsare na kasa, Prince Clem Agba, ya yi magana a kan gobarar da ta tashi a ofishin babban akawu na kasa inda ake zargin ta tafka barna a ginin ofishin na akawun gwamnatin tarayya.

Yace "Mu na wani taro na wasu ministoci da mambobin majalisa lokacin da labarin tashin gobarar ya same mu, kuma nan da nan na nemi a yi min uzuri don na garzayo na ga halin da ake ciki.

"Lokacin da na iso tuni jami'an hukumar kashe gobara na tarayya tare da hadin gwuiwar jami'an kashe gobara daga babbban bankin kasa (CBN) da jami'an kashe gobara na FCT da na wasu kamfanoni sun kashe wutar da ke ci.

"Gobarar ta fara ne da misalin karfe 10 na safe, wutar ta tashi ne sakamakon haduwar wayar wutar lantarki a wurin kunna na'urar sanyaya daki da wani jami'i ya kunna a hawa na hudu na benen gini."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel