Gwamnatin Kaduna ta gurfanar da Fastoci 2 gaban kotu saboda karya umarnin gwamna

Gwamnatin Kaduna ta gurfanar da Fastoci 2 gaban kotu saboda karya umarnin gwamna

Gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da kama wasu limaman coci coci guda biyu tare da gurfanar da su gaban wata kotun majistri sakamakon kamasu da ta yi da tara gangamin jama’a a cocinsu a ranar Lahadin da ta gabata.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jahar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka, inda yace an kama Fastocin ne a unguwar sabon tasha dake cikin karamar hukumar Chikun, inda suke keta umarnin gwamnan jahar na hana duk wasu taruka saboda gudun yaduwar Coronavirus.

KU KARANTA: An yi rikici tsakanin Yansanda da matasa a Kaduna, mutane 5 sun mutu

Gwamnatin Kaduna ta gurfanar da Fastoci 2 gaban kotu saboda karya umarnin gwamna
Gwamnatin Kaduna ta gurfanar da Fastoci 2 gaban kotu saboda karya umarnin gwamna
Asali: Twitter

Aruwan ya bayyana sunayen Fastocin kamar haka; Fasto Ifeanyi Ojonu da Fasto Giniki Okafor, wanda yace an gurfanar dasu gaban kotu a kan tuhumarsu da laifuka biyu da suka hada da hadin baki da kuma kin biyayya ga halastaccen umarni bisa sashi na 59 da 115 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Kaduna.

Aruwan ya kara da cewa an samu matsalolin rashin biyayya ga umarnin gwamnati na killace kai tare da kula da duk wasu hanyoyin kare kai daga kamuwa daga cutar Coronavirus, haka zalika ababen hawa na haya na cigaba da aiki a garin Kaduna, wanda hakan tasa gwamnati ta yi barazanar dakatar da sassauta dokar da ta yi niyya.

“Mun samu goyon baya da hadin kan kungiyoyin Musulunci, duka da yadda suka garkame Masallatansu na sallolin yau da kullum, da ma Masallatan Juma’a, haka zalika an rufe cocina da dama, amma akwai wasu limamai biyu da suka shirya sallar juma’a a ranar 27 ga watan Maris.

“Ba tare da wata wata ba aka kama su, kuma aka gurfanar da su gaban kuliya manta sabo a ranar 30 ga watan Maris, da wannan gwamnati ta nanata cewa babu wanda ya fi karfin doka, don haka zamu dabbaka dokar hana zirga zirga ba tare da tsoro ko son kai ba.” Inji shi.

Daga karshe Aruwan ya yi kira ga jama’an jahar Kaduna su tabbata sun kai karar duk wani jami’in gwamnatin jahar Kaduna ko kuma jami’in tsaro da ya ci zarafinsu ko kuma ya tauye musu hakkokinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel