Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 16, Jimilla 254
Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane goma sha shida (16) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2020.
Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma sha shida(16) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 10 a Legas, 2 a Oyo, 2 a Abuja, 1 a Delta, 1 a Katsina.“
“Kawo karfe 9:30 na yammacin 7 ga Afrilu, mutane 254aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami mutane 44, kuma mutane 6 a rigamu gidan gaskiya.“
DUBA WANNAN: Tashin hankali: Wani dan Najeriya mai Coronavirus ya gantsarawa ma'aikaciyar jinya cizo a fuska
Ga jerin jiha-jiha:
Lagos- 130
FCT- 50
Osun- 20
Oyo- 11
Edo- 11
Bauchi- 6
Akwa Ibom- 5
Kaduna- 5
Ogun- 4
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-2
Benue- 1
Ondo- 1
Kwara- 2
Delta- 1
Katsina-1
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng