An bayyana dukkanin addinai a matsayin abubuwan cutarwa da kuma hauka mutane a kasar Iceland

An bayyana dukkanin addinai a matsayin abubuwan cutarwa da kuma hauka mutane a kasar Iceland

- Kasar Iceland ta bayyana addinai da abubuwan cutarwa tare da takurawa ga dan Adam

- Kamar yadda rahoto ya bayyana, kasar Iceland ta haramtawa masu kira zuwa ga addinin Kirista shiga kasar tun a 2017

- A halin yanzu 'yan majalisar tarayyar kasar 60 ne suka goyi bayan sabuwar dokar inda uku kacal suka ki aminta da hakan

Kasar Iceland ta bayyana addinai da abubuwan cutarwa ga rayuwar dan Adam.

Kasar Iceland dai wani karamin tsibiri ne da ke Arewacin Atlantic. Majalisar tarayyar kasar ta amince da saka jan kunne ga dukkan masu amfani da Bibul a 2017 a matsayin masu tabin kwakwalwa.

A wannan shekarar kuwa, kasar ta dau wani mataki na haramtawa masu kira ga addinin kirista shiga kasar. A halin yanzu kuwa, Iceland ta bayyana dukkan addinai da tabin hankali.

An bayyana dukkanin addinai a matsayin abubuwan cutarwa da kuma hauka mutane a kasar Iceland
An bayyana dukkanin addinai a matsayin abubuwan cutarwa da kuma hauka mutane a kasar Iceland
Asali: Getty Images

Albingi, majalisar tarayyar kasar ta saka kuri'ar hakan inda aka qsamu kuri'u 60 me goyon bayan hukuncin. Uku ne kadai basu goyon bayan dokar. 'Yan siyasa ukun kuwa da suka soki hakan sun yarda cewa wannan dokar ba ta dace ba. "Bamu son komawa tamkar Amurka ko kasar Saudi Arabia, ko muna so?" Daya daga cikin dan majalisar da ya bukaci a boye sunan shi ya bayyana.

A wani labari na daban, Rundunar 'yan sandan kasar Afrika ta Kudu (SAPS) ta damke ango da amarya, fasto da kuma sama da 'yan biki 40 sakamakon karya dokar hana walwala ta kasar da suka yi. An kama su ne yayin da suke shagalin biki a Richard Bay, wani gari da ke KwaZulu-Natal.

'Yan sandan sun yi kamen ne yayin da ake tsaka da bikin kuma an tasa keyar mutanen ne zuwa ofishin 'yan sanda na Empangeni.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama ango da amarya da sauran 'yan biki da suka karya dokar hana fita da gwamnati ta saka

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar, Birgediya Vishnu Naidoo wanda ya tabbatar da kamen, ya ce masu gurfanarwar ne za su sanar da 'yan sandan hukuncin mutanen.

Naidoo ya ce: "Mutane na daukar komai da wasa. Basu duban hatsarin muguwar cutar. A halin yanzu, bana tunanin akwai dalilin tara jama'a don yin taron biki. Za mu tattauna da dukkansu don jin dalilin take doka.

"Za mu yanke musu hukunci don sun take doka wanda hakan ke da matukar hatsarin gaske. Masu gurfanarwar ne za su bayyana mana hukuncin da ya dace. Bana tunanin za mu bukaci wani bayani daga wajensu don kuwa sai mun zanta da babban jami'in gurfanarwa."

Ana tsammanin wadanda suka take dokar za su bayyana a gaban kotu nan da ranar 6 ga watan Afirilu.

A ranar 26 ga watan Maris na 2020 ne gwamnatin kasar Afirika ta Kudu ta bayyana dokar hana walwala ta kwanaki 21. Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya ce hakan ya zama dole don gujewa masifa da annoba. Ya kuma umarci rundunar sojin kasar da su tabbatar da an bi dokokin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel