An garkame dan takarar gwamnan jihar Legas saboda ya karya dokar da gwamnati ta sanya ta hana fita

An garkame dan takarar gwamnan jihar Legas saboda ya karya dokar da gwamnati ta sanya ta hana fita

- Tsohon dan takarar kujerar gwamnan jihar Legas, Gbadamosi Babatunde ya shiga hannun jami'an tsaron jihar

- Ana zargin tsohon dan takarar ne da halartar liyafar zagayowar ranar haihuwar Abdul-Rasheed Bello, mai gidan Funke Akindele

- Kamar yadda majiya daga hedkwatar jami'an tsaron ta bayyana, ba za a sako Gbadamosi ba har sai an kaishi kotu don fuskantar hukunci

Tsohon dan takarar kujerar gwamnan jihar Legas, Babatunde Gbadamosi, ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Legas sakamakon take dokar hana walwala da jihar ta gindaya.

An damke Gbadamosi ne bayan da aka ganshi a bidiyon liyafar zagayowar ranar haihuwar Abdul-Rasheed Bello, mijin 'yar wasan Nollywood, Funke Akindele. An yi liyafar ne a rukunin gidaje da ke Amen a Ibeju-Lekki da ke jihar Legas.

An garkame dan takarar gwamnan jihar Legas saboda ya karya dokar da gwamnati ta sanya ta hana fita
An garkame dan takarar gwamnan jihar Legas saboda ya karya dokar da gwamnati ta sanya ta hana fita
Asali: Facebook

Majiya daga hedkwatar jami'an tsaron ta bayyana cewa an tsare Gbadamosi kuma ba za a sake shi ba har sai an gurfanar dashi a gaban kotu, jaridar The Guardian ta ruwaito.

A wani labari na daban, Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya koka da yadda labaran bogi ke yaduwa a kan gwamnatin tarayya wanda hakan ke janye hankalinsu daga yakar muguwar cutar coronavirus a kasar nan.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Mohammed ya jajanta cewa akwai mutanen da ke dauke hankalin mulkin shugaba Buhari daga yakar muguwar cutar coronavirus, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

A yayin da yake bada misali, ministan ya ce: "Daya daga cikin labaran bogin kwanakin nan shine wanda aka ce babu yunwa a kasar nan kuma gwamnatin tarayya ta fitar da naira biliyan dari ga 'yan Najeriya. Labarin bogi ne kuma ni ban sanar da hakan ba."

Duk da cewa ministan bai fitar da sunaye ba, amma ya ce masu yada labaran bogin basu denawa.

"Wadanda suka shirya janye hankalin gwamnatin tarayya ta hanyar yada labaran bogi, suna yin haka ne don hana yakar annobar coronavirus kuma ba za su dena ba.

KU KARANTA: Coronavirus: Kasar Iran ta mayar da Masallaci kamfanin hada takunkumin fuska

"Sun yada cewa mambobin kwamitin shugaban kasar a kan yaki da coronavirus sun amince da wani salon raba duk gudumawar da ta iso. Wannan labarin bogi ne. Wadannan mutane sun shirya janye hankalin gwamnatin tarayya a kan yakar annobar coronavirus," yace.

Kamar yadda yace, dalilin da yasa gwamnatin tarayya ke jawabi kullum shine don sanar da 'yan Najeriya halin da ake ciki a kasar nan dangane da muguwar kwayar cutar.

Ya shawarci 'yan kasa da su gujewa labaran bogi tare da jaddada cewa duk labaran da basu fito daga kwamitin shugaban kasar ko ministan ba, na bogi ne.

"Dalili daya da yasa muke taron manema labarai kullum shine don sanar da 'yan kasa halin da ake ciki a kan barkewar annobar coronavirus. Duk wani labarin da bai fito daga bakin ministan ba ko kuma kwamitin shugaban kasar, kada a danganta mu da shi.

"Cibiyar yaki da yaduwar cutuka na kokarin bayani a shafinta na yanar gizo kuma za a iya samun labaran a wajensu.

"Wasu shafukan yanar gizo da aka san su da kwarewa a yada labaran bogi duk a gujesu. A dena sauraronsu," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel