Da duminsa: An sake sallamar mutane biyu bayan sun warke daga cutar Coronavirus

Da duminsa: An sake sallamar mutane biyu bayan sun warke daga cutar Coronavirus

Gwamnatin jihar Legas a ranar Litinin ta sanar da cewa an sake sallamar mutane biyu masu dauke da cutar Coronavirus bayan samun waraka a asibitin jinyar cututtuka dake unguwar Yaban jihar.

Gwamnan jihar Legas da kansa, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin Litinin, 6 ga watan Afrilu, 2020.

Yace: "Ina da karin labari mai dadi gareku daga asibitin jinyar cututtuka dake unguwar Yaba."

"A yau, yan mata biyu sun samu waraka daga cutar #COVID19 kuma an sallamesu daga asibitin."

"A yanzu muna da jimillar mutane 31 wadanda suka samu waraka daga cutar a jihar Legas kuma tuni dun koma gidajensu."

"Muna matukar godiya ga ma'akatan kiwon lafiyanmu bisa namijin kokarin da sukeyi a wannan lokaci mai wuya."

Da duminsa: An sake sallamar mutane biyu bayan sun warke daga cutar Coronavirus
Da duminsa: An sake sallamar mutane biyu bayan sun warke daga cutar Coronavirus
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Rabawa talakawa shinkafa, daukan ma'aikata 774,000 da sauran matakan rage radadi 7 da FG ta dauka

A bangare guda, Kwamitin kar ta kwana na yakar COVID-19 a jihar Kwara ta tabbatar da bullar cutar na farko a jihar. Mutane biyu aka tabbatar sun kamu da cutar. TVC News ta ruwaito.

Ta farko wata matar wani mara lafiya ne da ya mutu a asibitin koyarwan jami'ar Ilori ranar Alhamis; dayan kuma wani ne da ya dawo daga kasar Birtaniya.

Gwamnatin jihar ta saki jawabin ne misalin karfe 6:33 na yammacin nan yan mintuna bayan samun sakamakon gwajin daga cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya dake Ibadan.

Gwamnatin za tayi hira da manema labarai gobe (Talata) da safe misalin karfe 11 na safe domin cikakken bayanai kan matakan da ake dauka wajen dakile cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel