Nan zuwa watar Mayu, mutane 4500 zasu kamu da Coronavirus a Afrika - Masana Kimiyya

Nan zuwa watar Mayu, mutane 4500 zasu kamu da Coronavirus a Afrika - Masana Kimiyya

Nahiyar Afrika na iya fuskantar kamuwar mutane 450,000 da cutar Coronavirus a watan Mayu idan ba'a harzuka wajen gwada mutane da inganta harkokin kiwon lafiya ba.

Wasu masana kimiyya daga kwalejin gyaran muhalle da likitanci dake Landan sun bayyana hakan ne bisa ga binciken lissafi da suka gudanar kan yadda adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus ta ninku cikin mako daya kacal.

Kawo yanzu mutane 9,198 suka kamu da cutar a nahiyar Afrika, 813 sun warke kuma 414 sun rigamu gidan gaskiya.

Masana Kimiyyan sun yi hasashen cewa a gabashin Afrika kadai, kowace kasa dake cikinta zasu samu akalla mutane 10,000 nan da 10 ga watan Mayu.

Kasashen da ke gabashin Afrika sune: Djibouti, Eriteria, Ethiopiya, Kenya, Madagascar, Mauritius, Ruwanda, Seysheles, Somaliya, Sudan, Tanzaniya, Uganda da Sudan ta kudu.

Yayinda cutar ta bulla a kasashe 51 cikin 56 na nahiyar, masanan sun bayyana cewa kawai matakin da za'a iya dauka domin hana wannan hasashe shine idan mutane suna nisanta da juna.

Shugaban masana masu binciken, Carl Pearson, ya bayyana cewa: "Mu kawai hasashe mukeyi da yanayi bullar a yanzu. Amma idan aka gudanar da gwajin sosai za'a fi saurin sanin adadin nan."

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara biyan N20,000 ga wasu talakawa 84,000 da suka fito daga kananan hukumomin jihar Kano 15

Nan zuwa watar Mayu, mutane 4500 zasu kamu da Coronavirus a Afrika - Masana Kimiyya
Nan zuwa watar Mayu, mutane 4500 zasu kamu da Coronavirus a Afrika - Masana Kimiyya
Asali: Facebook

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Kaduna ta ce kawo yanzu an tura sanfurin jinin mutane 89 Abuja domin gwaji.

Kwamishanar kiwon lafiyan jihar, Dakta Amina Mohammed Baloni, wacce ta bayyana hakan ranar Litinin ta ce cikin samfura 89 da aka tura, sakamakon ya nuna 5 sun kamu, 77 basu kamu ba, kuma ana sauraron 8.

Baloni a jawabin da ta saki ranar Litinin ta ce kawo yanzu an katabta sunayen mutane 119 da ake nema.

Tace: "Gwamnatin jihar na dauka tsauraran matakai wajen dakile yaduwar cutar COVID-19 tun watan Febrairu ta hanyar tuntubar shugabannin asibitocin jihar kan yadda za'a shawo kan lamarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel