Annobar Corona: Gwamnatin Katsina ta umarci ma’aikata su koma bakin aiki

Annobar Corona: Gwamnatin Katsina ta umarci ma’aikata su koma bakin aiki

Gwamnatin jahar Katsina a karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari ta umarci kafatanin ma’aikatan gwamnati da su koma bakin aikinsu daga ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu.

Legit.ng ta ruwaito gwamnatin ta sanar da haka ne cikin wata wasika dake dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jahar, Alhaji Idris Usman Tune dauke da kwanan watan 5/04/2020.

KU KARANTA: Buhari ya gargadi Sojoji da su kauce ma cin zarafin yan Najeriya saboda dokar ta-baci

Annobar Corona: Gwamnatin Katsina ta umarci ma’aikata su koma bakin aiki
Annobar Corona: Gwamnatin Katsina ta umarci ma’aikata su koma bakin aiki
Asali: Facebook

Sanarwar ta bayyana cewa: “Biyo bayan matakin da gwamnatin jahar Katsina ta dauka na umartar ma’aikatun gwamnatin jaha da na kananan hukumomi su zauna a gida domin kiyaye yaduwar cutar COVID-19,

"Amma a yanzu bayan gudanar da nazari tare da duba shawarar masana, Gwamna Aminu Bello Masari ya umarci ma’aikatan gwamnati su koma bakin aiki daga ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, 2020.

“Ma’aikatan za su gudanar da ayyukan da ba’a rasa ba daga karfe 10 na safe zuwa karfe 2 na rana, za’a cigaba da haka tsawon mako daya cur. Amma dukkanin makarantun gaba da sakandari, na sakandari na kudi da na gwamnati za su cigaba da zama a kulle har sai yadda hali ya yi.

“Haka zalika ana kira ga ma’aikata da su kasance suna dabbaka ka’idar kauce ma shiga cunkoson jama’a, tsayawa nesa nesa da juna, wanke hannuwa da kuma amfani da sinadarin Sanitizer don tabbatar da an kare bullar COVID-19 a Katsina.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wasu rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani kasurgumin dan bindiga mai garkuwa da mutane a jahar Katsina mai suna Abdulhadi Dan Nashe, kamar yadda jaridar Katsina Post ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa Dan Nashe ya gamu da ajalinsa ne a hannun yaransa bayan sun yi masa bore, sun juya masa baya sakamakon wata rashin fahimta da aka samu a tsakaninsu.

Majiyar ta kara da cewa dalilin wannan rashin fahimta da ya kunno kai a tsakanin yan bindigan baya rasa nasaba da wata tirka tirka da ta taso tsakanin Dan Nashe da matarsa, wanda ita kan kanwa ce ga wani shugaban yan bindiga, mai suna Dangote.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel