Gwamnatin jihar Neja ta janye dokar hana fita, ta umurci ma'aikata su koma aiki gobe

Gwamnatin jihar Neja ta janye dokar hana fita, ta umurci ma'aikata su koma aiki gobe

Gwamnatin jihar Neja ta janye dokar ta baci da ta sanya a jihar inda aka haramtawa mutane zirga-zirga saboda tsoron yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

A yanzu, an amince mutane su fita harkokinsu daga karfe 8 na safe zuwa 2 na rana.

Sakataren gwamnatin jihar kuma shugaban kwamitin kar ta kwanan yakin Coronavirus, Ahmed Ibrahim Matane, ya sanar da hakan ne a Minna, yayin hira da manema labarai kan matakan da gwamnatin ke dauka wajen dakile cutar.

Ya ce za'a bude kasuwanni daga karfe 8 zuwa biyu kuma ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki amma zasu tashi karfe 2.

Ahmed Ibrahim ya kara da cewa gwamnatin ta gano hanyoyi 12 da mutane daga wasu jihohi ke iya shiga Neja kuma za'a cigaba da rufe iyakokin jihar.

Har yanzu Jihar Neja bata cikin jerin jihohin da akasamu bullar cutar a Najeriya.

KU KARANTA: Saba dokar hana fita: Jami'an tsaro sun damke motoci 51, babura 46 a Abuja

Gwamnatin jihar Neja ta janye dokar hana fita, ta umurci ma'aikata su koma aiki gobe
Gwamnatin jihar Neja
Asali: Facebook

Wannan ya biyo bayan sake waiwayen da gwamnatin jihar Bauchi tayi kan wata sanarwa da ta fitar na sanya dokar ta baci da zata rufe jihar na tsawon kwanaki 14 domin dakile shiga da yaduwar cutar Covid-19 (coronavirus) a fadin jihar, inda ta ce yanzu ta sassauta zuwa rufe iyakokin jihar kawai.

Janye wannan kudiri na sanya dokar ta baci a jihar, zai baiwa al’ummar jihar damar ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, wadanda tuni suka fara shirin killace kawunansu a gidajensu na tsawon makonni biyu.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, Shugaban Kwamitin dakile yaduwar cutar Covid-19 a jihar, kuma mataimakin gwamnan jihar, Sanata Baba Tela, ya shaida cewa gwamantin ta yi dogon nazarin halin da jama'a za su fada a sakamakon hana su zirga-zirga da harkokinsu na yau da kullum.

Jihar Bauchi ce jiha ta shida cikin jerin jihohi mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel