Yanzu-yanzu: Mutum daya ya sake warkewa daga Coronavirus, an sallameshi

Yanzu-yanzu: Mutum daya ya sake warkewa daga Coronavirus, an sallameshi

- Tabarkallah! An samu karin Mutum daya da ya samu waraka daga muguwar cutar Coronavirus da ta addabi duniya

- Gwamnan jihar Legas ya bayyana cewa sun sallami marasa lafiyan a ranar Asabar

Wani mai fama da cutar Coronavirus dake killace a asibitin cututtuka dake Yaba, Legas ya samu lafiya kuma tuni an sallamesa.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai ranar Asabar.

Gabanin yanzu, an sallami mutane 22 bayan an tabbatar da sun warke daga cutar cikin 109 da suka kamu da cutar a jihar. Mutum daya kadai ya mutu.

A fadin tarayya kuwa, cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa a yanzu, mutane 209 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami 26 , kuma hudu ya rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Mutane 7 kacal suka halarci daurin auren diyar gwamnan Jigawa (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Mutum daya ya sake warkewa daga Coronavirus, an sallameshi

Mutum daya ya sake warkewa daga Coronavirus
Source: UGC

A bangare guda,Mutumi mai shekaru 55 a duniya da ya mutu a asibitin koyarwan jami'ar jihar Legas LUTH, Idi Araba, sakamakon cutar Coronavirus bai fadawa ma'aikatan kiwon lafiya gaskiyar abinda yake fama da shi ba lokacin da aka kai shi asibiti.

Majiya a asibitin ya bayyana cewa sai bayan mutuwarsa aka gudanar da gwaji aka gano cewa yana dauke da cutar Coronavirus a jikinsa.

Hakazalika masu jinyarsa suka ki bayyanawa asibitin ainihin abinda ke damunsa da kuma irin tafiye-tafiyen da yayi zuwa kasar waje a makonni baya-bayan nan.

"Amma bayan mai rijistan asibitin ya bayyana masa abubuwan da suka gano a jikinsa, mutumin ya bayyana gaskiyar cewa lallai da yiwuwan ya kamu da cutar COVID-19 saboda tafiyar da yayi kasar waje."

"Ya bayyana cewa tun lokacin da ya dawo daga kasar Holan makonni biyu da suka shude yake fama da tari." Cewar majiyar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel